Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi alkawarin sake gina hanyar Saminaka zuwa Marjire da ke karamar hukumar Lere a jihar, wanda ambaliyar ruwa ta raba gida biyu.
Ya ce, a sakamakon ruftawar hanyar, an katse al’umma biyar daga hedikwatar karamar hukumar zuwa sauran sassan jihar.
- Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Miyagun Kwayoyi A Kano
- Fashewar Tankar Mai: Minista Ya Jajanta Wa Al’ummar Neja Da Iyalan Mutum 59 Da Suka Mutu
Gwamna Sani ya bayar da wannan tabbacin ne ta bakin shugaban ma’aikatan jihar, Sani Kila, inda ya ce, gwamnatin jihar za ta dauki matakin gaggawa domin magance matsalolin da al’ummar yankin ke fama da su da ma daukacin karamar hukumar Lere.
Kila, wanda ya jagoranci tawagar kwamitin yaki da ambaliyar ruwa zuwa yankin, ya ci gaba da cewa, gwamnatin Uba Sani ta himmatu wajen bunkasa tattalin arzikin karkara.
Baya ga sake gina wani bangare na hanyar da ta rufta, za a bai wa mutanen al’ummomin da abin ya shafa kayayyakin agaji.
Shugaban karamar hukumar Lere, Hon. Mathew Bulus Gambo, ya bayyana godiya ga Gwamna Uba Sani bisa kafa kwamitin mai karfi wanda shugaban ma’aikatan jihar ke jagoranta, yana mai cewa, hakan na nuni ne da jajircewar Gwamnan na magance matsalolin da jama’a ke fuskanta.
Kwamitin ya kuma ziyarci wasu wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa a cikin karamar hukumar, ciki har da kauyen Wawan Rafi, inda wata gada ta rufta, da yankin Nasarawa, da Ungwan Shuru a cikin garin Saminaka.