Manajan Darakta na kamfanin bunkasa ma’adanai a Kaduna, Injiniya Shuaibu Kabir Bello, ya sanar da cewa a kwanan nan ne kamfanin ya gano albarkatun ma’adanai daban-daban har 73 a duk fadin jihar, wanda wannan gagarimin ci gaba ne da ke shirin canza yanayin tattalin arzikin Kaduna.
“Da wannan arzikin ma’adanai, za mu samar da dubban guraben ayyukan yi ga matasa a fadin Jihar Kaduna. Wannan damar za ta samar da ci gaba tare da fata da wadata ga matasanmu, “in ji shi.
- EFCC Ta Kama Matashi A Kaduna Bisa Zargin Wulaƙanta Naira A Bidiyon Barkwanci
- Za Mu Magance Matsalar Ruwan Sha Kafin Ƙarshen 2025 A Kaduna – Uba Sani
Bello ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar kamfanin da ke Kaduna. Ya bayyana cewa kamfanin a shirye yake don daukar matakai masu tsauri wajen jawo hankalin masu saka hannun jari da habaka bangaren hakar ma’adanai.
Ya bayyana cewa Jihar Kaduna tana da albarkatun ma’adanai iri-iri, ciki har da zinariya, tagulla, azurfa, bakin karfe da sauransu.
Da yake jaddada muhimmancinsu, Bello ya ce, “Muna da komai daga zinariya, tin, tagulla, azurfa, bakin karfe, bakin dutse, Lithium da dai sauransu, Lithium wani muhimmin bangare ne na canjin makamashi na duniya.”
Ya kara da cewa bukatar kasa da kasa game da karfin ma’adinai na Kaduna yana karuwa, tare da masu saka hannun jari da yawa wadanda suke bincike kan yadda za su yi amfani da wadannan albarkatun da ba a taba amfani da su ba.
“Baya ga wannan, muna da ma’adanan karfe. Kamfanin ‘African Mines’ ya riga ya zo Kaduna don hakar wannan albarkatun, wanda ya nuna a fili cewa Kaduna tana da ma’adanan karfe da za a iya gudanar da kasuwancinsu,” in ji shi.
Bello ya jaddada cewa tsarin kamfanin yana nuna jajircewa don kokarin killace iyakokin ma’adinai da kuma habaka su.
Ya ce tun lokacin da aka kafa kamfanin, hukumar gudanarwaar kamfanin ta ba da fifiko ga ayyukan da ke sanya alhakin muhalli da zamantakewar al’umma a gaba a ayyukanta.
Haka kuma manajan daraktan ya kuma yaba wa Gwamna Uba Sani saboda goyon bayan da yake bayarwa ga bangaren hakar ma’adanai, yana mai cewa a karkashin jagorancin gwamnan, kamfanin ba wai kawai a shirye yake ba har ma yana da cikakkiyar kayan aiki don samar da sakamako mai kyau.
“Ana sa ran wannan kokari zai samar da ci gaba a hakar ma’adanai tare da bude hanyoyin arziki a bangaren ma’adanai, samar da dubban ayyuka, da kuma habaka ci gaban tattalin arziki ba kawai a Kaduna ba har ma a duk fadin Nijeriya,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa masu saka hannun jari na cikin gida da na waje samar da yanayi mai aminci wanda ke karfafa kirkire-kirkire da ci gaba na dogon lokaci.
Bello ya kuma sanar da cewa kamfanin bunkasa ma’adanai na Kaduna a shirye yake ya yi maraba da masu saka hannun jari da ke da sha’awar yin amfani da albarkatun kasa na jihar.
Ya bayyana tashar sarrafa lithium ta Kangimi, wacce ke aiki a karfin tan 5,000 a kowace rana, a matsayin babban ci gaba a tafiyar hakar ma’adinai ta jihar.
“Bisa jajircewar kamfanin wajen samar da aminci da ci gaba mai dorewa, Kaduna za ta kasance a matsayin babban wurin saka hannun jari,” in ji shi.
Ya nuna godiya ga Gwamna Uba Sani, yana mai cewa, “Godiya ga kokarin da Gwamna Uba Sani ya yi, muna shaida canji mai ban mamaki a bangaren hakar ma’adanai wanda ke bude hanya don kyakkyawar makoma mai kyau.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp