Masu sharhi kan harkokin siyasa na ciki da wajen Nijeriya idanunsu sun karkata kan majalisar ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kafa.
An dai ayyana Shugaba Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya ne bayan ya lashe zaben da aka gudanar a watan Fabrairu wanda a halin yanzu ake kalubalantarsa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da dan takarar jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar kuma dan takarar jam’iyyar LP, Mista Peter Obi.
An ci gaba da ce-ce-ku-ce kan shugabancin Tinubu kan yadda ‘yan Nijeriya ke fatan ganin wa’adin mulkinsa ya kai ga ci gaban al’ummar kasar bayan da ya cimma burinsa na rayuwa na shugaban kasar Nijeriya.
Tuni dai Shugaba Tinubu ya dauki kwararan matakai dangane da maye gurbin shugabannin hukumomin tsaro da dakatarwar da ya yi wa gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele da kuma na shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, amma har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na cikin kokwanton kan abubuwan da suke tsammani ga Shugaba Tinubu.
A wurin bikin rantsuwa na ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shi mai cin gajiyar goyon baya ne da kuma fatan mai kyau ga al’ummar Nijeriya, inda ya yi alkawarin ba zai ci amanar miliyoyin ‘yan Nijeriya ba.
A wata hira da jakadar kasar Ingila a Nijeriya, Richard Montgomery, ya bayyana cewa Ingila na jiran Shugaba Tinubu ya kafa majalisar ministocinsa domin daukar matakan da suka dace wajen karfafa dangantakar tattalin arziki da Nijeriya.
Montgomery ya bayyana cewa gwamnatin Burtaniya ta gano wasu bukatu shida wadanda kasashen biyu za su iya karfafa hadin gwiwa da kuma gina sababbin wuraren da za a ci moriyar juna.
Jakadar ya ce Birtaniya ta fi sha’awar kara alakar kasashen biyu kamar yadda Tinubu ya bayyana a baya-bayan nan game da shawarwarin tattalin arziki.
“Muna da dadaddiyar alaka mai cike da tarihi kuma muna da ginshiki mai karfi da za mu gina, sannan ina da kwarin gwiwa game da alkiblar Nijeriya a cikin shekaru masu zuwa.
“Muna fatan inganta dangantakarmu ta fuskar tattalin arziki, musamman game da matakin farko da sabuwar gwamnati ta yanke ya nuna cewa za ta dauki manyan matakai kan tattalin arzikin da nake ganin za su ba mu damar bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari.
“Kuma ina ganin akwai fannoni da dama da gwamnatin Burtaniya za ta iya inganta harkokin diflomasiyya bisa alakarmu da Nijeriya. Amma ko shakka babu, muna jiran nadin sabbin ministoci domin mu sami damar tattaunawa ta diflomasiyya da ta dace don shimfida dangantaka,” in ji Montgomery.
A bangare guda kuma, kungiyar habaka tattalin arzikin Arewa (AEC) ta bukaci Shugaban kasa Tinubu kar ya ba da fifiko wajen nada mukaman ministoci.
Shugaban kungiyar, Ibrahim Yahaya Dandakata shi ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.
Ibrahim ya kara da cewa shugaban kasa na iya tabbatar da cewa an dora wa mutane nagartattun mutane alhakkin yi wa kasa hidima ta hanyar sanya cancantar a sahun gaba wajen yanke shawarar wadanda za a bai wa mukamin ministoci.
“Nijeriya tana fama da matsalolin tattalin arziki, zamantakewa da siyasa, wanda hakan ya haifar da matsalolin da suka shafi kasar baki daya, kamar yawan rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki da ba a taba ganin irinsa ba, da rashin hadin kan ‘yan kasa lamarin da ya haifar da rashin tsaro a wasu sassan kasar nan.
“Nada mutanen da suka cancanta da suka dace suke da hazaka da kwazo da iya aiki wani muhimmin mataki ne na samun ingantaccen jagoranci da shugabanci. Nijeriya ta samu kanta a wani mawuyacin hali kuma dole ne shugabanni su kasance suna da wadannan siffofi a maimakon a mayar da hankali kan siyasa da son zuciya.
“An zabi shugaban ne bisa karfin aikinsa a matsayinsa na dan siyasa kuma shahararren dan kasuwa. An dai shaide shi da rikon gaskiya da amana a wajen kula da dukiyar al’umma.
“Muna kira gare shi da ya ci gaba da kiyaye wannan abin da ya gada tare da fito da kyakkyawan tsari na gwamnatinsa da kasa baki daya. Kamar yadda aka yi la’akari da nade-naden mukamai da suka hada da na ministoci da sauran mukamai, muna karfafa wa shugaban kasa gwiwa da ya yi la’akari da kwarewa da cancanta fiye da komai,” in ji Ibrahim.
Ita ma kungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN), ta kuma shawarci Shugaba Tinubu da ya nada ministan wutar lantarki mai nagarta wanda ba ya cin hanci da rashawa ke da kwarewa sosai a bangaren wutar lantarki.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Darakta Janar na MAN, Mista Segun Ajayi Kadir, inda ta ce nasarar da dokar samar da wutar lantarki ta shekarar 2023 da shugaban kasa ya sanya wa hannu za ta ta’allaka ne kan aiwatar da shi yadda ya kamata da kuma nada kwararre a fannin fasaha.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp