Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Mai Martaba Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana kafafen sada zumunta (Social media) a matsayin “Ƙungiyar ‘yan ta’adda” da ya zama dole a yi gaggawar magance ta domin kiyaye tsaron kasa.
Da yake jawabi yayin taron kwamitin zartarwa karo na 17 na Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da aka gudanar a Maiduguri na Jihar Borno a ranar Talata, Sarkin Musulmi ya koka da yadda kafafen sada zumunta ke ta yaɗa labaran ƙarya da tada zaune tsaye a faɗin ƙasar nan.
- ‘Yan Ta’adda Sun Tarwasta Gadar Mandafuma A Jihar Borno
- An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia
“Abin da ya faru ya riga ya faru, amma in ya biyo ta hanyar kafafen sada zumunta – kungiyar ta’addanci …,” in ji Sultan.
“Abin da suke yi … wani zai zauna a ɗakinsa ya tsara labarai ta yadda za ku yi tunanin cewa gaskiya ne, don haka, wannan kafar watsa labarai, kamar ƙungiyar ta’addanci ce wacce ya kamata a yi maganinta. Dole ne hukumomin tsaro su magance wannan ƙungiyar ta’addanci da ake kira ‘social media’.”
Sultan ya bayyana matukar damuwarsa kan taɓarɓarewar tsaro a sassan kasar nan, musamman a jihar Filato, inda hare-haren baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba dubbai da muhallansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp