A yau Laraba 22 ga watan Janairu, kafar CMG ta kammala gwajin shagalin bikin bazara na shekarar 2025 da ta shirya kuma za ta watsa. Shagalin bikin ya kunshi wakoki, da raye-raye, da wasan kwaikwayo na “opera”, da wasu shirye-shirye masu kayatarwa da ban sha’awa, an kuma hade su da juna yadda ya kamata.
Kaza lika, an tsara sassan ayyukan nuna shagalin bikin bisa matukar kwarewa. Bikin na cike da abubuwa masu faranta rai, da ba da dariya, da yanayi mai karfi na bikin sabuwar shekarar ta Sinawa. (Saminu Alhassan)