Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, manufar Sin daya tak a duniya, ita ce ta ke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.
Mao Ning ta bayyana hakan ne Litinin din nan, a yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, tana mai cewa, “Muna shirye don samar da yanayi mai kyau na dinkuwa cikin lumana, amma ba za mu taba barin wata kafa da ‘yan aware za su gudanar da ayyukan ‘yancin kan Taiwan ba.” (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp