Annabi tsira da amincin Allaah sutabbata agate shi yana cewa: “kuyiwa juna kyauta za’a so ku”, mutane suna son wanda zai basu abin dunia, wannan ya sa Allaah ya shar’anta bada zakka ga wanda ake fatan shigarsa Musulinci, kamar yadda ya zo a suratu Attaubah, Manzon tsira ya bawa wasu dukia don su tabbata a Musulinci, Imaaninsu ya inganta.
Duk mai kudin da yakeyiwa mutane kyauta dawuya suyi masa hassada, kullum za su dinga murna da ganinsa, suna masa fatan alkhairi.
Idan muka duba suratun Namli zamu ga lokacin da Alhud-huda ya jefawa Bilkisu Sarauniyar sabi’i wasika wacce ta kunshi wajabcin mika wuya ga Annabi Sulaiman, ta shawarci mutananta game da matakin da ya kamata a dauka, sun bata shawarar ayi amfani da karfi, amma ita kuma sai ta ce zata aikawa da shugaba sulaiman kyauta, saboda ta San kyauta tana sanyaya zukata, ta kuma kusanto sa da kusa.
Annabi tsira da aminchin Allaah su tabbata a gare shi yana cewa: “Nakasance cikin bukatar dan ‘uwana shi yafi mini alkhairi fiye da na yi’itikafi a wannan masallacin nawa.”
Sai dai duk haka Allaah yayi dan’Adam da son dukia, wannan ya sa baya iya jure roko, in muka duba Al-kur’ani ko Allaah in zai tambayi zakka ko sadaka yakan gorantawa mutane, a cikin suratun Nuur “Kuma kubasu daga dukiar da Allaah yaba ku” a suratun Nisa’i yace ;
“Kuma an sanyawa zucia kwauro” Idan zai bi muminai yakan ce, kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su.
“Dayanku yayi sammako ya yo icce a bayansa, ya yi sadaka da shi ya kuma wadatu daga mutane, shiyafi masa daya tambayi wani mutum ya ba shi ko ya hana shi, hannun dayake bayarwa yafi hannun da yake amsa, ka fara da wanda kake daukar nauyi.” Duk wanda yakeson zaman lpia toh karya yadinga rokon mutane wani abu, wani mawakin larabawa yana cewa; “Allaah yana fushi idan kadaina rokon sa, shi kuma dan’Adam lokacin da kake rokonsa yake fushi.”
Annabi tsira da amincin Allaah su tabbata agare shi yayi alkawari da wasu daga cikin sahabbansa karsu roki kowa wani abu, don haka bulalar daya daga cikinsu takan fadi yana kan abin hawansa amma bazai ce amiko masa ba, sai dai ya sauko da kansa ya dauka. Yawancin yan’Adama basa son bambadanci, an ruwaito hadisi cewa ; “In kanason mutane su so ka, toh ka guji abin da yake hannunsu” wani Balarabe yana cewa ; “Idan za’a tambayi mutane tur6aya, su durkusa su ya fito su baka, da sunce bazasu bada ba, Muhammadul Amin Ash-Sahankidi wanda ya rasu a shekara ta 1393 H yan cewa: “Nazo da wata taska daga wadda da wuya ka samu wanda yake da irinta, ita ce :dangana da wadatar Zuci” Haka haka malami magabata suke.
Ada’u dan abi Rabah- daya daga cikin malamai magabata nagari -bawa ne aka ‘yanta shi, Baki ne, ana cewa yana da siffofi na muni, yana da shanyayyen hannu, yana da cin zan-zana, amma lokacin da suka hadu da sulaiman Bn Abdil-Malik daya daga cikin halifofin daular Umawiyya wanda yaga mahaifinsa a shekara ta 99, kuma a shekarar ya mutu, ya hadu da Ada Bin Abi Rabah a harami, sai ya ce masa: “Malam ka tambayeni duk abinda kake so” sai Ada’u ya ce; “Dan jirani, Inaso zanje nayi dawafi”, yajira shi yaje yayi dawafi ya fito. dayafito sai yasake maimata masa tambayar: “Ka tambaye ni duk abinda ka keso.” Sai yace masa “Wallahi har nashiga na fito ban roki Allaah ko abu daya na dunia ba, don haka kaima bazan tambaye ka ba.”
Haka Hisham Bin Abdil-Malik, shi ma daya ne daga cikin halifofin Daular Umawiyya, sun hadu da Bajimin malami Salim dan Abdallah dan Umar a masallaci, ya ce masa: “Allaah ya gafarta Malam, in kana da bukata ka tambaya a yi maka.” Sai yace; “Wallahi ina jin kunyar na tambayi wanda ba Allaah ba a masallaci” saboda haka bayan an gama sallah sai ya fita waje ya jira shi a wajen masallaci.
Da suka fito sai ya sake maimata masa waccar maganar a wajen masallaci, ya ce : “Duk abin da kake so ka fada a maka” sai ya ce masa: “Har nagama nafito daga masallacin ban roki Allaah komai na dunia ba, saboda haka tunda ban roki Allaah ba, kai ma bazan rokeka ba.”
Haruna Ar-rashid wani lokaci ya gama aikin hajji, sai ya ce a dan zagaya da shi wajen malamai su yi masa wa’azi, duk malamin da ya je gurinsa sai ya tambaye shi: ana bin ka bashi? Sai ya ce: “EH”, sai a dau jakar kudi a ba shi, har suka je gurin Fudhail Bin Eyadh ya ce ya masa wa’azi, sai ya yi masa wa’azi mai shiga jiki. Sai ya fashe da kuka, yayi ta ruri.
Bayan ya gama sai ya ce da Fudhail dan Eyadh: “Ko ana bin ka bashi? Sai Fudhail Bin Eyadh ya ce: “Eh, akwai bashin da ake bi na in za ka iya biya, akwai bashin da na dauko a gurin Allaah na farillai da sunnoni, su ne ba na iya biyan su yadda ya kamata, idan za ka iya biya sai ka biya min”, ya shiga cikin gida yayi ta kuka. Baiwarsa ta ce: Ina ma ka dan kar6i wani abu, tunda Muna cikin talauci, ka gazai taimaka mana.
Ya yi ta rusa ruri, ita da kanta ta fito waje ta ce da Haruna Ar-rashid: “Don Allaah ka tafi, saboda ka cutar da bawan Allaah nan. A lokacin fa shi Haruna Ar-rashid shine shugaban duniar musulmai baki daya.
Mawallafi: Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Bita: Dr Abdul-kadir Isma’il, Bayero Unibersity kano