Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, a yau Jumma’a ta soki ikirarin da Amurka ta yi na cewa tafarnuwa ta kasar Sin na da “babbar barazana” ga kariyar abinci a Amurka, tana mai cewa, masu amfani da yanar gizo na kasar Sin sun yi wa wadannan kalamai ba’a.
A cewar rahotanni, dan majalisar dattawan Amurka, Rick Scott a baya-bayan nan ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa, tafarnuwa ta kasar Sin tana da “babbar barazana” ga kariyar abinci a Amurka, ya kuma yi kira da a kaddamar da bincike na sashe na 301. Kana majalisar wakilan Amurka ta yi nazari tare da zartas da “dokar ba da izinin tsaron kasa ta sabuwar shekarar kasafin kudi ta shekarar 2025”, wadda kuma ta hada da tanade-tanade da ke bukatar shagunan sojin Amurka hana sayar da tafarnuwar kasar Sin.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 181, Sun Cafke 203 A Cikin Mako Guda – Hedikwatar Tsaro
- Shugabancin Nijeriya: ‘Yan Arewa Ku Jira Har Zuwa 2031 —Sakataren Gwamnatin Tarayya
“An yi imanin cewa tafarnuwa ba ta taba tunanin za ta iya haifar da babbar barazana ga Amurka ba,” a cewar kakaki Mao Ning a taron manema labarai yayin da take mayar da martani ga tambayar da ta shafi batun.
Ta kuma bayyana cewa, akwai karuwar salon likawa kayayyakin kasar Sin lakabi, kama daga jiragen sama marasa matuka, da injina na crane, daga firij zuwa tafarnuwa, a matsayin “barazana ga tsaron kasa,” yayin da babu daya daga cikin wadanan dalilan da ’yan siyasar Amurkan suka nakalto da zai iya jure wa bincike.
Kakakin ta kara da cewa, a bayyane yake ga kowa da kowa cewa irin wadannan ayyuka tamkar wata hujja ce kawai ga Amurka don neman kariya ga kasuwarta, da yin amfani da ikon gwamnati wajen murkushe ci gaban kasar Sin, da dakile ci gaban da kasar Sin ke samu, da kuma yin yunkurin wargazawa tare da tarwatsa tsarin masana’antu da tsarin samar da kayayyaki. (Mohammed Yahaya)