Kwanan nan ne wasu ‘yan siyasa, gami da kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya, suka bayyana cewa wai tattalin arzikin kasar Sin yana tafiyar hawainiya, al’amarin da ka iya haddasa hatsari ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya karyata wannan furuci a yau Laraba 16 ga wata, abun da a cewarsa, ya sabawa gaskiya.
Wang ya ce, tattalin arzikin kasar Sin na kara murmurewa, wanda hakan ke zama muhimmin karfi ga habakar tattalin arzikin duniya. Ya ce a farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan karuwar GDPn kasar Sin ya kai kaso 5.5 bisa dari, wanda ya zarce na bara wato kaso 3 bisa dari, kana ya zarce matsakaicin yawan karuwar GDPn kasar na tsawon shekaru 3, yayin da ake fama da annobar COVID-19, wato kaso 4.5 bisa dari.
Kaza lika asusun bada lamuni na duniya IMF, ya fitar da wani sabon rahoto a watan da ya gabata, game da hangen nesa kan yanayin tattalin arzikin duniya, wanda ya nuna cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kaso 5.2 bisa dari a bana, lamarin da zai bayar da gudummawar kaso 1 bisa 3 ga karuwar tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)