Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya sanar da janye ƙudurin dokar da ya gabatar na tilastawa mutane jefa ƙuri’a—wanda ya haifar da cece-kuce.
A cikin wata sanarwa da mataimakinsa na hulɗa da Jama’a, Musa Abdullahi Krishi, ya fitar da ita a ranar Litinin, Shugaban ya bayyana cewa “bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, ya yanke shawarar janye ƙudurin gyara dokar zaɓe ta 2022 don sanya jefa ƙuri’a ya zama dole ga duk ƴan Nijeriya da suka cancanta.”
- Tabbas Amurka Za Ta Cije A Yakin Haraji Da Ta Kaddamar A Duniya
- A Tsammaci Garambawul Ga Dokar Zabe Kafin Zaben 2027 — Shugaban INEC
Ya yi nuni da cewa an gabatar da dokar ne da niyya mai kyau,
“don ƙarfafa shigar da jama’a cikin zaɓe da haɓaka dimokuradiyyarmu ta hanyar ƙara yawan masu jefa ƙuri’a.”
Sanarwar ta kara da cewa, “A wasu ƙasashe kamar Brazil, ana tilasta jefa ƙuri’a, kuma hakan ya taimaka wajen samun fiye da kashi 90 cikin 100 na masu jefa ƙuri’a, yayin da ƙasashe kamar Argentina da Singapore su ma suka aiwatar da irin wannan matakin don haɓaka shigar da jama’a cikin zaɓe.”
Shugaban ya amince da cewa doka ta shafi jama’a, kuma dole ne ta mutunta ‘yancin ɗaiɗaikun mutane da ra’ayinsu.
Maimakon tilastawa, ya ce zai mai da hankali kan ƙarfafawa da fito da sabbin hanyoyin da za sa jefa ƙuri’a ya zama abin sha’awa da sauƙi ga duk ƴan Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, “Janyewar wannan dokar zai ba da damar ƙarin tattaunawa kan mafi kyawun hanyoyin haɓaka al’adar jefa ƙuri’a don raɗin kai, wanda zai mutunta aƙidar dimokuraɗiyya da kuma haƙƙin ƴan ƙasa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp