Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen ya taya mabiya addinin kirista murna a lokacin da suke gudanar da bukukuwan Kirsimeti, wanda ke nuna ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Abbas, yayin da yake yi taya kiristoci bukukuwan Kirsimeti, ya ce haihuwar Yesu Kiristi na nufin sabuntawa da cikawa yayin da ya kuma yi kira da a sake jaddada fata ga kasa a wannan mawuyacin lokaci na rayuwar ‘yan Nijeriya.
- Canada Za Ta Caka Wa Kanta Wuka Kan Matakin Da Ta Dauka A Kan Kasar Sin
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 14 A Jihar Filato
A cikin sakon taya murna da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Abdullahi Krishi ya fitar, shugaban majalisar ya bukaci Kiristoci da ‘yan Nijeriya baki daya da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa sabuwar Nijeriya addu’a ga kowa da kowa.
Ya kuma yi kira da a yi wa kasa da shugabanninta addu’o’i, musamman shugabannin siyasa da na addini da masu rike da sarauta.
Shugaban majalisar ya kuma yi kira da a hada kai da zaman lafiya da kaunar juna duk da bambancin addini da harsuna da ke tsakanin ‘yan kasar.
Ya bayyana fatan nan ba da jimawa ba Nijeriya za ta zama kasa abin alfahari ga kowane dan kasa.