Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya bayyana alhini da kaɗuwa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana mai bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan Nijeriya ‘yan kishin ƙasa da aka taɓa samu.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa bayan sanarwar rasuwar tsohon shugaban ƙasar a Landan a sakamakon gajeriyar rashin lafiya, Abbas ya ce Buhari, wanda ya rasu yana da shekaru 82, ya sadaukar da yawancin rayuwarsa wajen hidimtawa ƙasar nan.
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
Kakakin ya bayyana Buhari a matsayin soja kuma dattijo wanda ya kafa suna da matsayin shugaba mai gaskiya da rikon amana, wanda rayuwarsa ta kasance cike da sauƙi da rashin kwaɗayin abin duniya da kyakkyawan ɗabi’u da suka sa aka yarda da shi sosai a fadin ƙasa.
Abbas ya ce Buhari yana daga cikin mutane biyu kacal da suka shugabanci Nijeriya a matsayin soja da kuma shugaban ƙasa a mulkin dimokuraɗiyya (bayan Olusegun Obasanjo), lamarin da ya ce wata dama ce ta musamman.
Abbas ya ambaci irin ƙaunar da talakawa musamman a Arewacin Nijeriya ke yi wa Buhari a matsayin ɗan siyasa, yana danganta hakan da dabi’unsa na gaskiya.
Kazalika, Abbas ya bayyana yadda Buhari da wanda ya gada shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu suka kafa jam’iyyar APC, har lamarin ya yi ƙarfin da ya karɓe mulki daga PDP a 2015, bayan shekaru 16 suna mulki.
Abbas ya ce akwai jimami cikin rasuwar Buhari, bayan shekaru takwas a kan mulki, yanzu ya koma ga Allah domin hutu na har abada.
Kakakin ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari da Sarkin Daura da al’ummar Daura da gwamnatin Jihar Katsina, har ma da Jihar Kaduna inda Buhari ya kwashe mafi yawan rayuwarsa yana zaune.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp