Kakakin ofishin jakadancin Sin a Amurka, ya soki lamirin damar da Amurka ta baiwa jagorar yankin Taiwan, na bi ta cikin kasar yayin da take bulaguro, inda har ta samu zarafin ganawa da kakakin majalissar wakilan kasar Kevin McCarthy.
Kakakin ofishin jakadancin na Sin, wanda ya yi tsokaci kan batun a ranar Laraba, ya ce shigar Tsai Ing-wen cikin Amurka, tare da ganawa da Kevin McCarthy matakin watsi ne da kashedin da kasar Sin ta sha yi kan hakan.
Jami’in ya ce Amurka ta keta hurumin manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin hadin gwiwa 3 da sassan biyu suka amincewa. Har ila yau Amurka ta yi watsi da alkawarin da ta yi don gane da batun Taiwan, ta kuma aike da mummunan sako ga masu rajin samun ‘yancin yankin na Taiwan.
Sakamakon hakan, kasar Sin ta soki matakin da kakkausar murya, tana kuma matukar adawa da shi, kana za ta dau matakin da ya dace da wannan keta ka’ida da Amurka ta yi.
Har ila yau, jami’in ya kara da cewa, ba wani sashe da zai iya dakatar da manufar dinkewar dukkanin sassan kasar Sin. Kuma tarihi zai shafe masu neman goyon bayan Amurka game da burin su na “Samun ‘yancin kan yankin Taiwan”. Bugu da kari, masu amfani da yankin Taiwan da nufin sarrafa akalar kasar Sin za su gane cewa “Kan su suka hakawa ramin mugunta”.
A Juma’ar nan ne ofishin lura da harkokin yankin Taiwan na kwamitin kolin JKS, ya sanar da kakaba takunkumi kan dan-gani-kashenin burin “Cin gashin kan Taiwan” mai suna Bi-khim Hsiao. Kaza lika ofishin ya bayyana hukunci kan wasu kungiyoyin yankin, da suka hada da “Prospect Foundation”, da “Council of Asian Liberals and Democrats”, bisa zargin su da yayata manufar “Neman ‘yancin Taiwan”. (Saminu Alhassan)