Kalamai dai ma`anarsu, furuci ne da baki, na wasu maganganu kiyayya kuma su ne, kishiyar soyayya, ko kauna, idan ba ka san kiyayya ba, to ana nufun kishiyar kyauna, ko so, misali kishiyar zaki shi ne daci, to wannan kalma mai harufa bakwai kacal, yin ta ga wani mutum ko wata al`umma, ta siyasa ko ta kabila, kalma ce mai nauyi, da ke haddasa rigingimu da tashin hankali a duniya.
Domin kowa duk inda aka yi wannan kalama, to ba shakka da zarar an yada, to abu ne, da ke kawo matsala a kowace irin kasa a duniya, kamar yadda labaran karya da yada jita-jita ke hadasa wa.
- Dalilin Haramta Wa ‘Yan Adaidaita Sahu Bin Manyan Tituna – Gwamnatin Kano
- An Tsinci Gawar Wani Dan Kasuwa Mai Shekaru 37 A Otel A Jihar Bauchi
Dan haka ne ma, za ka ga cewa, misali abu na farko da ake karantar da dan jarida tun a matakin farko, shi ne iya bakinsa ta hanyar kauce wa kalamai na bata wani mutum ko wata kabila ko kungiyar wasu mutane ko mabiya wani addini da suka yi imani da shi.
Idan ban manta ba, kuma in na fahimta a karatuna na jarida a tsakanin makarantar koyan aikin jarida da ke karkashin hukumar AME a kano, da karatuna na BUK da ni yi karatun jarida cikin cokali, a shekarun da suka wuce, akwai dokoki da dama a darasin da ake cewa “PRESS LAW” ko kuma “Communication Law” a cikin wannan darasi akwai maganar wani abu da ake ce wa “Defamation” wanda ke nufin ka da ka bata sunan mutum, ko aibata shi da daraja, ko kimarsa ta zube. Wannan kuma na san ana karantar da ‘yan jarida ne bisa la`akari da yadda aikinsu na rubutu a jarida ko a karanta a rediyo da talabijin,da sauran kafafn yada labarai.
Wannan kuwa dole a ba shi horan iya magana don kauce wa kalaman kiyayya ko yada su, Kamar yadda yake faruwa a halin yanzu.
Kyakkyawan misali na illar kalaman kiyayya da yada su da tarihin duniya ba zai manta da shi ba, shi da ya faru a daya daga cikin kasashen Afrika wato kasar Ruwanda a shekara ta1988, tsakanin kabilar Hutu da Tutsi, inda aka kasha dubban muta ne, wanda ba su ji ba ba su gani ba, wanda an ce ko a rana daya an kashe mutum dubu 100 wannan fa ba wani abu ba ne ya jawo shi ba, sai kalaman kiyayya da yada su.
An ce, Kalmar ta faro ne daga wani mutum na cewa AKASHE KYANKYASAI ita ce aka yi amfani da ita a tsakanin kabilar Hutu da Tutsi manyan kabilu ne a kasar masu rinjaye da marasa rinjaye a cikinsu bayan harbo jirgin shugaban kasa da ya fito daga daya kabilar ta Ruwanda, da aka yi a kasar duk dai kalaman kiyayya ne da yada su ta jawo wa kasar Ruwanda wannan masifa, wanda yanzu ya wuce ya zama tarihi da ba a fatan irinsa ko maimaita shi a ko’ina cikin duniya.
Akwai bukatar ya zama darasi ga ‘yan Nijeriya musamam ‘yan siyasa da na ji a kwananan wata jami`a a ofishin jakadancin Birrtaniya ta yi kashedi na hana me yin wannan shiga kasarta kalamun da ka iya kawo wa dimakaradiyya cikas a Najeriya.
Haka kuma idan ka koma can baya a tarihi za ka ga cewa an yi yake-yake a duniya musali idan ka dau tarihi na Larabawa da za ka ga cewa an yi yake- yake tun kafun zuwan addin Musulunci, wanda ba wani abu ba ne ya hadasa irin wadanan yake-yake sai kalamai na kiyayya da yada shi a tsakanin mawaka da masana fanin ke cewa mawakan jahiliya, da sauransu inka dawo baya kadan za ka ga cewa an yi yaki tsakanin kasar Amurka da kawayenta wajan yakar kasar Iraki idan ka karanta tarihin wannan yaki da aka fara a 1991 za ka ga asalin wannan yaki a faru ne daga kalamai na rashin fahimtar juna a tsakanin su wanda za ka iya kiransa da kalaman kiyayya da yada shi.
Kafin mu dawo gida Nijeriya dan ba da misali da abubuwa na tashin hankali da suka faru a kasashe wani abu da za ka iya kira da kalaman kiyayya ne ya hadasa su a kasashen Turai, Duniya ba za ta manta da abun da aka yi ba na yakin duniya na daya da yakin duniya na biyu ba, ko ba a cema kalaman kiyayya ne suka hadasa wannan ba to ba ka ce ko kalaman soyayya ba ne, ko kauna ce ta hada sa yakin duniya na daya da na biyu ba, in ko ba haka ba ne ya zama kalaman kiyayya Ke nan.
Ka dubi abubuwan da suka faru na siyasar duniya a tsakanin kasashen yammacin Turai da tarayar Sobiyat, tsakanin yan kwamnis da yan jari huja na cacar-baka na shekara da shekaru, da ya kawo karshe bayan rushewar tarayar Sobiyat, da sauransu. Ka da mu manta da wata kalma da ake kira da turanci Crusade tana cikin tarihi duniya mana dadi, har yanzu ba mai san tu na ta ko amfani da ita a duniya.
Tarihin Nijeriya ba zai kammala ba sai ka sa maganar yakin Biyafara, a kano sai kasa tarihin yakin mai tatsine, da sauran rigingimu na siyasar NEPU da NPC wanda ya gangaro har zuwa maganar santsi tabo duk wadanan da aka yi ba sunansu zaman lafiya ba duk da sun zama tarihi amma an san ba kalaman yabo ko kauna ce ya kawo wadanan rigingimu ba, kishiyar kalaman so ne da kauna ya kawo wadanan rigingimu.
Wani musali na kwananan shi ne yanzu haka wata koto a kasar nan, na tuhumar wani matashi dan asalin jahar jigawa, mai suna Aminu Adamu kan zargin kalaman batanci da yada kiyayya ga uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafafan sada zumunta da aka zargi matashin da yin hakan, kuma wani abu mai kama da haka ya faru a Kaduna tsakanin wani malami da wani dan siyasa kuma tsowan soja daya zargi malamun da kalaman kiyayya a kansa inda sai a gaban koto aka warware wannan matsala tsakanin wani malami da wani tsohon soja a Kaduna kamar yadda kafafan yada labarai suka ba da labia a lokacin.
Abubuwa da daman a rashin fahimtar juna na da yawa wanda kalaman kiyayya da yadasu ke hadasawa ko rikicin gida da ake yi tsakanin kishiya da kishiya ko makoci da makoci ko aboki da aboki da direba da direba akan hanya da makamantansu ba kalaman suyayya ne suke hada su ba.
Kuma wannan kalma ta kiyayya kishiyar soyayya ta fi zafi a yanzu haka musammam ga yan siyasa wanda kuma babbar masifa ce da ya kamata a kauce ma a wannan lokaci da mu a Najeriya ake sauran kwanaki kasa da 90 dan shiga runfunan zaban shugaban kasa, da sanatoci, wakilan tarayya, gwamnoni da yan majalisar jaha a tarayar Nijeriya.
Duk dai wannan kalma ta kiyayya ba ta da tasiri sai an yada ta a kafafan yada labarai wanda kuma yanzu haka babban kalubalan da ke gaban mu shi ne yanzu na kafofun sada zumunta na zamani da kuma wasu gidajen rediyo da sauran wasu kafafn yada labarai wadanda ko dai basu horo na aikin yada labarai, ko kuma san zuciya ya danne huran da karatunsu na ba sa aiki da shi, kuma wannan babban kalubale ne, na a guji wadanan kalamai na yada kiyayya da yin ta wannan kuma ya hada da wuraran tarowa da yin lakcoci ko huduba, a masalatai da ma jami`u a guji yin kalaman kiyayya da kuma yada su ta kafafan yada labarai, domun su ne kanwa uwar gami wajen ya ya ta abun da zai kawo zaman lafiya ko akasain ha ka wato kishiyar haka a Nijeriya dama duniya baki daya dan haka dole a yi hatara!
Wata na siha da zan karkare wannan rubutu da ita ita ce nasihar da daya daga cikin malamai a wani lokacin a wata hira muka yi da shi a kwanakin baya inda Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar, OON ya yi na cewa kalaman kiyayya da yadashi da jita jita addini bai yadda da shi ba, inda ya ce wajibi ne su limamai su guji yada kalamai wadanda za su tunzura jama`a a Mambarurunsu na huduba inda ya ce ko da mutum ba dai dai ya ke ba to munin aikin za a fada ba a nu na masa kiyayya ba, domun anga irin masifun da irin wadanan abubuwa su ka jawowa duniya dan haka wajibi ne a isar da sako cikin hikima kamar yadda aka koyar mana a lidafun Allah mai tsarki, kuma a guji yada labaran karya ko yada kiyayya karya, da jita jita ba su taba zama alkairi a rayuwa.
Mustapha Ibrahim, Wakilin LEADERSHIP Hausa ne, ya rubuto daga Kano