Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar shugaban Amurka, Donald Trump, kan tura sojojin ƙasarsa zuwa Nijeriya don yaƙar ta’addanci abun damuwa ne da ya kamata ya tayar wa kowa hankali.
Obi, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya ce kowane ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa dole ne abin da ke faruwa ya dame shi.
Ya ce, “Babu shakka matsalar tsaro ta addabi Nkjeriya, wadda ta jawo mutuwar mutane da dama da asarar dukiya. Rahoton Amnesty International ya nuna cewa sama da mutum 10,000 aka kashe tun watan Mayu 2023. Wannan lamari abin takaici ne kuma dole ne gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa.”
Obi ya ƙara da cewa, matsalar tsaro za ta iya samun mafita ne idan aka samu shugabanci na gari.
“Ko da yake ba wannan gwamnati ce ta haifar da matsalar ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin tsayayyen mataki daga wannan gwamnatin ta APC wajen magance ta,” in ji shi.
Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya da Amurka na da kyakkyawar alaƙa tun da daɗewa, don haka bai kamata wannan sabuwar dambarwa ta lalata dangantakar ƙasashen biyu ba.
Obi ya ce dole ne a yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen shawo kan matsalar.
			




							








