Daya daga cikin jarumai mata masu tasowa a masana’antar Kannywood jaruma Fatima Abdullahi, ta bayyana batutuwa da dama dangane da rayuwarta a masana’antar ta shirya fina finan Hausa, daga zuwanta masana’antar samun daukakarta ta kuma kalubale da yau da kullum da ta fuskanta a tsawon lokacin da ta shafe a Kannywood.
Fatima a wata hirar da ta yi da DCL Hausa ta bayyana cewar duk da cewar ana kallonta a fina-finan da ta ke fitowa amma dai yawan dora hotunanta a kafafen sada zumunta shi ne ya janyo mata daukaka, saboda tarin mutane da ke bibiyarta a kafar sada zumuntar, ina yawan samun likings da engagements a duk lokacin da na dora hotona a shafina na Facebook da sauran wurare in ji Fatima.
- Idris Ya Musanta Rahoton Wai Ya Ce A Yi Watsi Da Koken Gwamna Zulum Kan Rashin Tsaro A Borno
- NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya
Fatima Hussaini yar asalin Suru da ke Jihar Kebbi a Nijeriya ta yi suna a lokacin da ta taka rawar gani a cikin shirin Labarina, Fatima wadda ta fito a matsayin karamar jaruma a fim din ta burge mutane da dama sanadiyar rawar da ta taka, musamman wadanda ke sha’awar kallon fina finan Hausa.
Da ake tambayarta a kan kalubalen da ta fuskanta a yayin da ta ke sabuwar shiga masana’antar Kannywood Fatima ta ce zuwa yanzu dai babu wani abu da za ta iya bayyanawa a matsayin kalubelen da ta fuskanta, sai dai kuma ba za a rasa yan kananan matsaloli na yau da gobe ba.
A kan nasarorin da ta samu kuwa Fatima ta ce akwai dimbin nasarori da ta samu kasancewarta jarumar masana’antar Kannywood, duk da cewar ba komai ne za ta iya fadi ba amma dai fuk wanda ya sanni bara ya san cewar na samu canji sosai hakazalika akwai wurare da na shiga sanadiyar fim wanda idan ba ta hanyar fim din ba ba lallai bane in iya shiga ta ce.
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp