A kwanan baya ne, asusun da ke tallafa wa kananan yara na Majalisar dinkin Duniya wato UNICEF, ya bayyana cewa,’yan Nijeriya sama da miliyan 95 ba a samar masu da kayan kulawa da muhalli ba.
Wannan adadin ya nuna yadda a zahiri ake ci gaba da fuskantar kalubalen rashin kula da kiwon lafiyar al’ummar kasar nan.
- Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Kamfanin Tsaftace Haƙora A Arewacin Nijeriya
- Akwai Bukatar Mu Bai Wa Mbappe Lokaci Domin Dawowa Kan Ganiyarsa – Ancelotti
A gafe daya kuma, ana ci gaba da fuskanar matsalar dabi’ar yin bahaya a fili tare da matsalar rashin samar da kayan da za a rinka kulawa da muhalli a kasar.
Wannan kididdigar ta kara jefa fargaba a cikin zukatan al’umma da kuma karya wa jama’a kwarin Gwiwa.
Babban abin takaici anan shi ne, yau a Nijeriya kimanin ‘yan kasar kimanin miliyan 48 ciki har da yara kimanin miliyan 18, sun rungumi dabi’ar yin bahaya a fili.
Kazalika ma, wannan matsalar har ta kai ga ta zama wata babbar annobar da ke shafar kiwon lafiyar jama’a, shafar ilimin su na zamani da kuma bunkasar tattalin arzikin al’ummar kasar, inda wannan kalubalen har ya kai ga zarce fiye da tunanin dan Adam. Bugu da kari, wasu makarantun gwamnati a kasar, da cibiyoyin kula da kiwon lafiya, musamman na gwamnatin, wadanda ya kamata ace, ana samar da inganataccen ilimin zamani su kuma cibiyoyin kiwon lafiya yadda ya kamata, amma abin bakin ciki, sun kasance tamkar kufai, saboda rashin wadata su da kayan aiki.An kiyasata cewar, makarantun Boko na gwamnati guda 91,000 da kuma cibiyoyin kula da lafiyar ‘ al’umma guda 7,600, ba a tanadar masu da kayan aiki na tsaftace muhalli ba. Hakanan ma, akan wadannan alkaluman an kiyasata cewa, ana bukatar a kalla Naira biliyan 168.75, domin a magance yin bahaya a fili a Nijeriya.
Sai dai kuma, abin takaici, anan shi ne daga shekarar 2018 zuwa 2022, Naira biliyan 15 ne kacal, aka kashe wajen magance yin bahaya a fili, wanda wannan adadin ko rabin Naira biliyan 168.75, ba su kai ba.
A jawabinsa na kwanan baya, mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya danganta matsalar wacce ta kara rashin tsaftar muhalli, inda ya shawarci daukacin gwamnonin jihohin kasar, da su kara zage damtse a kan kokarin da suke yi na wayar da kan al’umomin su domin a kawo karshen kalubalen yin bahaya a fili, nan da shekaru biyar masu zuwa.
Kashim ya kuma kara da cewa, wayar da kan al’umma na da matukar mahimmanci, domin ta hakan ne tamkaran dauki wani mataki na kawo karshen yin bahaya a fili, wanda hakan kuma zai inganta kiwon lafiyar ‘yan Nijeriya.
Kazalika ma, domin a yaki wannan dabi’ar ta yin bahaya a fili, gwamnatin tarayya ta samar da wani shirin tsaftace Nijeriya mai taken ‘Yin Amfani Da Bandaki Domin Wayar Da Kai.
Sai dai kash!, abin bakin cikin shi ne, ya zuwa yanzu dai, wannan shirin ya fara tafiya ne da kafar hagu saboda kuwa, a kananan hukumomi 17 a cikin dari kacal ne wannaan shirin ya samu nasara, inda kashi tara daga cikin dari, wanda jihohin kasar ke samun tallafin UNICEF.
Tun a shekarar 2023 ne gwamnatin tarayya ta samar da dauki na samar da kayan aikin kulawa da muhalli.
A namu ra’ayin a nan shi ne, dole ne gwamnonin kasar nan su dauki wannan lamarin da matukar mahimmanci.
Gudanar da gangamin wayar da kai kan batun na bukatar matukar a mayar da hankali ta yadda ya kamata, musamman a matakin gwamnatin tarayya.
Bugu da kari, ya zama dole suma sauran matakan gwamnati na jihohi da kuma kananan hukumomi, su zuba hannun jari a batun kare muhalli saboda a samar a makoma mai kyau ga Nijeriya a nan gaba.
Wata babbar illa ga rayuwar jama’a ita ce yin bahaya a fili na shafar ruwan sha da kuma yada cututtuka a cikin al’umma, tare da janyo illa ga rayuwar mata da ‘yan mata.
Kazalika, matsalar na kuma shafar fannonin ilimin zamani da tattalin arziki.
Sai dai, wata jami’a a UNICEF Rebecca Gebriel, ta na da yakinin cewa kafin nan da shekara ta 2030, daukacin jihohin kasar nan a karkashin shirin muradun karnin za su cimma burin su na yakar yin bahaya a fili.
Amma kafin a cimma wannan burin akwai matukar bukatar al’umma, kungiyoyi, kamfanoni masu zaman kansu, su sadaukar da kai.
A namu ra’ayin muna ganin ya zama wajibi ne a zuba hannun jari wajen samar da kayan tsaftace muhalli a illahirin kasar nan.