Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris, ta zabi gwamnan Jihar Minnesota, Tim Walz a matsayin wanda zai zama mata mataimaki a zaben shugaban kasa.
Wasu mutane uku da ke da cikakkiyar masanaiya kan lamarin ne, suka tabbatar da hakan a ranar Talata.
- Kasar Sin Za Ta Gina Sabon Tsarin Samar Da Wutar Lantarki
- Xi Ya Nanata Bukatar Kare Al’adu Da Kayayyakin Gargajiya Na Sin
Walz, wanda Gwamna ne mai ci kuma tsohon soja, ya taka muhimmiyar rawa wajen kare ‘yancin zubar da ciki.
A tarihi, babu wani dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar Republican da ya taba lashe jihar Minnesota ba tun bayan shekarar 1972, amma Donald Trump da gangamin yakin neman zabensa ya ce za su lashe jihar a wannan karon.
Walz, ya shiga gangamin yakin neman zaben na Harris ne a wani lokaci mai sarkakiya a tarihin siyasar Amurka.
Kusan daukacin ‘yan jam’iyyar Republican sun nuna goyon baya ga Trump bayan da aka yi yunkurin halaka shi a watan Yuli.
Makonni kadan bayan hakan, Shugaba Joe Biden ya janye takararsa, lamarin da ya sa Harris ta karbi ragamar tafiyar da jam’iyyarsu ta Democrat musamman wajen hada kan ‘ya’yanta.