Assalamu alaiku wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Masu karatu kafin mu shiga sabon darasinmu na Siffofin Annabawa, za mu karasa darasin da muke yi a game da Tsoron Allah da Ibadar Annabi (SAW).
Ausu dan Malik ya ce, wani dare na kasance tare da Annabi (SAW), sai ya farka ya yi Asiwaki sannan ya yi Alwala ya fara Sallah, ni ma sai na zabura na yi Alwala na bi shi, sai ya fara da Suratul Bakara kuma ba ya shige wata ayar Rahama sai ya tsaya ya roki Ubangiji tabaraka wata’ala in kuma ayar azaba ce sai ya tsaya ya nemi tsarin Ubangiji har sai da ya kai karshen Surar sannan ya yi Ruku’u. Gwargwadon nisan tsayuwar da ya yi, irin shi ya sake yi a Ruku’un, sannan ya karanta zikri a ruku’un yana ce wa “Subhana zil jabaruti wal malakuti wal kibriya’u wal azamati – tsarki ya tabbata ga ma’abocin rinjaye mai dimbin yawa, tsarki ya tabbata ga mai iko kuma mai jin Mulki da girma” sannan ya yi sujada sai ya taso kuma ya sake karanta Suratu Ali Imrana gaba dayanta a raka’a ta biyu, sannan ya dinga karanta sura bayan sura. Wannan sunnar Annabi ce kowanne dare kuma haka sahabbansa suka koya. Wasu daga cikin Sahabban Annabi (SAW) sun tafi cewa, dadewa a sujada ya fi wasu kuma suka ce tsayuwa ya fi.
- Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-17 Dauke Da ’Yan Sama Jannati
Akwai wani jikan Annabi (SAW) da ake kira da ‘Sajjadu’ sabida yawan sujadarsa ga Ubangijinsa, wata rana wani sarki ya daure shi a kurkuku amma yana da taga da yake ganin cikin kurkukun, kullum sarki ya farka bacci da hasken rana sai ya ga kamar an shanya wani bakin zani, wata rana sai ya tambaya, shi mai wancan bakin zanin kullum sai ya jika shi ne ya shanya? Sai aka ce masa, ai Sajjadu ne ya yi sujada har yanzun bai dago ba. Wannan tafiyarsa, sujada ta fi. Sayyadina Usman bin Affan shi kuma tsayuwa ta fi a mazahabarsa.
An karbo hadisi daga Sayyada A’isha ta ce, Annabi (SAW) wata rana ya tsaya da aya guda ta Kur’ani daren gaba daya. Wata kila an ce, Ayar “in tu’azzibhum fa’innahum ibaduk, wa in tagfirlahum fa’innaka antal azizul hakim – ya Ubangiji, in ka azabtar da su, duk bayinka ne, in ka gafarta musu daman kai mabuwayi ne mai hikima” a wata ruwaya, a karshen ayar Annabi (SAW) yana cewa, Ummati wata ruwaya kuma an ce, bai ji Ubangiji ya gafarta wa Al’ummarsa ba sai karshen Dare lokacin Sahur, A’rifai kuma suka ce, hikimar maganar ita ce “sabida dadin maganar da hikimar da ke cikin maganar ya sa, Annabi (SAW) ya yi ta maimaita maganar har karshen dare”.
An karba daga Abdullahi dan Mushakkiyyun yana cewa, na zo wurin Annabi (SAW), sai na same shi yana Sallah, sai na ji cikinshi yana kugi kamar akwai yunwa a cikin.
Dan Abi Halata ya fada, Annabi (SAW) ya kasance kusan kowane lokaci yana cikin Damuwa (Damuwar Al’ummarsa) da Tunani.
An karba daga Sayyadina Aliyu, yana cewa, na tambayi Annabi (SAW) game da aikinsa, sai ya ce “Sanin Allah shi ne kan dukiyata, hankali shi ne asalin addinina, soyayya ita ce ginshikina, shaukina zuwa ga Allah, Ambaton Allah shi ke dauke min kewa, dogarona ga Allah shi ne taskata, Ilimi shi ne makamina, Hakuri juriyata, yarda da Allah ganimata, gajiyawa ta alfaharina, Gaskiya kuma ita ce mai ceto na, biyayya ga Allah ta isar min, Jihadi kuma dabi’ata, sanyin Idona na cikin Sallah.” A cikin wani Hadisi kuma, an ruwaito “’ya’yan itatuwan zuciyata, suna cikin Zikirin Ubangiji, damuwar zuciya da nake ciki don al’ummata ne, shaukina kuma zuwa ga Ubangijina”
Annabi (SAW) ya ce, ba za ku shiga Aljannah ba sai kun yi soyayya, shin ba zan koya muku yadda ake soyayya ba? Ku dinga yin sallama a junanku, ciyar da abinci a tsakaninku, yin sallar dare sai Allah ya haskaka zuciyarku ta yi haske.
Darasi A Kan Sifofin Annabawa
Kamannin Annabawa suna tukewa ne kan siffofin Annabi Muhammadu (SAW), Siffofin Annabi (SAW) suna tukewa ne zuwa ga siffofin Rabbul Izzati. Halitta wata abu ce wacce mutum ba yadda zai yi ya iya kara ta ko rage ta, kamar Tsawo da Gajarta, dabi’a kuwa, mutum yakan iya tsururinta ta hanyar zama a wuri ko ibada da Ma’arifa da son Allah sai mutum ya yi haske, duk wanda ya rike Annabi (SAW) sai ya haska, duk wanda ya rike littafin Allah da gaskiya sai ya haskaka, duk wanda ya rike shari’ar Annabi (SAW) ba da Fitina ba sai ya haskaka, duk wanda ya rataya da abin da ya rataya da Annabi (SAW) sai ya haskaka sabida Annabi (SAW) Haske ne – “Hakika haske (Annabi Muhammad (SAW)) ya zo muku daga Ubangijinku”. Haka siffofin Annabawa suke ga Annabi (SAW) haka kuma suke ga Waliyyan Allah. Wani Sahabin Shehu Ibrahim Inyass (RA) yana cewa, in kana so ka ga siffofin Annabawa irin wacce aka ruwaito, ka ga Shehu Ibrahim Inyass, duk za ka ga wadannan dabi’u.
Fifiko gaba daya ya tattara ga Annabawa aminicin Allah ya tabbata a gare su, su suke da daukakar daraja amma duk da haka, Allah ya fifita wasu a kan wasu, Allah Ubangiji ya fada, “wadannan Manzonnin, mun Fifita wasu a kan wasu, wasu daga cikinsu Allah ya yi magana da su (Annabi Muhammad (SAW) kuma ya Fifita wasu a kan wasu”.
Ya zo a cikin Hadisin Annabi (SAW), “Farkon jama’ar da za ta shiga Aljannah, haskensu kamar na Wata dan daren 14 yake, kuma duk ‘yan Aljannah a bisa siffar mutum daya za su shiga Aljannah – Annabi Adam, tsawonsa kamu 60”
Annabi (SAW) ya ce, na ga Annabi Isah (AS) a ranar Isra’i, Mutum ne mara kwari amma dogo, mai sakakken gashi, mai dogon karan hanci, ya yi kama da Larabawan Yamen, yana da wata alama a fuskarsa, gashinsa kamar ya futo daga gidan wanka a lokacin.
Annabi (SAW) ya ce, ni kuwa, ni ne mafi kamar ‘ya’yan Annabi Ibrahim da Ibrahim, ranar Isra’i kamarmu daya, sai dai wannan yaro ne wannan tsoho ne.
A cikin wani Hadisi kuma, Annabi (SAW) ya fada a cikin tarihin Annabi Musa, na ga Annabi Musa kamar mutum mafi kyau da za ka gani, na daga mutum Ja ko wankan tarwada.
Ya zo a cikin wani Hadisi daga Abi Hurairata, ya karba daga Annabi (SAW), yana cewa, Allah bai aiko wani Annabi ba bayan Annabi Ludu face sai ya kasance a cikin mafi kololuwar dangi yadda ba zai tabu daga mutanensa ba (Ba bu wanda ya isa ya taba shi).
Turmizi ya ruwaito Hadisi daga Katadata, daga Anas ya ce, “Allah bai taba aiko wani Annabi ba sai mai kyawun fuska, mai kyawun murya”. Anas yake cewa, don haka, Annabi (SAW) ya fi duk Annabawa da Manzonni kyawun fuska da murya.
A cikin hadisin Hirakla, sarkin Rum, a hirarsa da Abi Sufyan ya ce “… na tambaye ka dangin Annabin nan (Annabi Muhammad (SAW) sai ka gaya min, shi ma’abocin dangi ne, dama haka Annabawa suke, ana aiko su a cikin babban dangi don su tsare shi.”
Allah tabaraka wata’ala ya fada cikin Annabi Ayyuba AS, “madalla da bawan nan namu, shi mai yawan komowa wurinmu ne”, ya fada cikin hakkin Annabi Yahya da cewa, “Ya Yahya, ka rike Attaura da karfi, mun ba shi Annabta tun yana Yaro, shi kuma rahma ne daga gurinmu, kuma sadaka ne ga halitta, mai tsoron Allah ne. Mai bin Iyayensa ne, bai kuma zama Azzalumi ba mai sabo. Amincin Allah ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da ranar da zai mutu da ranar da za a tashe shi, ranar tsayuwa” – kadan daga cikin rahma daya tak ta Annabi (SAW) kenan.