Taron COP28 da ke gudana a birnin Dubai ya cimma matsaya daya wajen fara aiki da asusun biyan asarar sauyin yanayi, ko kuma“Loss and Damage” Fund a Turance, don taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi. Hadaddiyar daular Larabawa, da Jamus sun yi alkawarin samar da kudi har dalar miliyan 100 kowaccen su, yayin da adadin da Birtaniya za ta bayar ya kai kimanin dalar miliyan 50.Amma Amurka wadda ta kan bayyana kanta a matsayin kasa dake matukar sauke nauyin dake wuyanta wajen tinkarar wannan matsala, ta yi alkawarin samar da dala miliyan 17.5 ne kacal, duk da cewa yawan hayaki mai dumama yanayi da take fitarwa gaba daya ya fi na ko wace kasa a duniya.
Amurka da dai sauran kasashen yamma, sun kwashe shekaru fiye da dari suna raya masana’antu, wanda hakan ya samar musu da arziki, da bunkasuwar tattalin arziki mai wadata, amma a sa’i daya, sun yi amfani da makamashi da albarkatu mafiya yawa, tare da fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da yawa, hakan ya sa dole ne wadannan kasashe su dauki alhakin bullar matsalar sauyin yanayi.
- Sin Ta Dauki Alhakinta Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi
- Kasar Sin Za Ta Soke Harajin Kwastam Da Ta Buga Kan Kaso 98% Na Hajojin Wasu Kasashen Afirka 6
Rahotanin da MDD ta bayar na nuna cewa, tun lokacin da aka fara Juyin juya halin masana’antu, kashi 58% na karuwar zafin yanayi da ayyukan bil Adama ke haifarwa, ya faru ne sakamakon abubuwan dumama yanayi da aka fitar kafin shekarar 1990, kuma daga shekarar 1850 zuwa 2019, yawan iskar Co2 da nahiyar arewacin Amurka da Turai suka fitar ya kai kashi 23%, da 16% na dukkan duniya. Amma abin takaici ne, kasashe maso tasowa ne suke fi fama da illar da sauyin yanayi ke haifarwa. Shugaban taron COP28 Dr. Sultan Al Jaber ya ce, wasu kasashe marasa karfi, musamman ma kasashe kananan tsibirai, da kasashe mafiya rauni, suna fama da illar sauyin yanayi mai tsanani.
Kamata ya yi, kasashe masu ci gaba sun sauke nauyin dake wuyansu na samar da kudade, don taimakawa wadannan kasashe wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi, don samar da daidaito da adalci a fannin yanayi,. Bai kamata kasashe masu tasowa su yi asara sakamakon bunkasuwa, da wadatar da kasashe masu wadata suka samu ba. (Mai zana da rubuta: MINA)