Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ziyarci asibitin koyarwa na Barau Dikko domin jajantawa da kuma tallafawa wadanda harin bam ya rutsa da su a Kaduna.
Mun rahoto muku cewa, mutane fiye da 90 ne suka mutu wasu kuma suka jikkata sakamakon harin da sojojin Nijeriya suka kai a daren Lahadi a kauyen Tudun biri, wanda sojojin suka ce kuskure ne.
- Gwamnan Sakkwato Zai Saya Wa Kansa Motocin Biliyan Daya
- Jami’an NDLEA Sun Yi Artabu Da Miyagu A Jihar Edo
Mataimakin shugaban kasar, tare da rakiyar jami’an gwamnati, ya yi rangadi a dakunan asibitin, inda da kansa ya gana da wadanda suka jikkata da kuma ‘yan uwansu da ke cikin damuwa.
Talla
Ya yi kalamai na jaje tare da ba su tabbacin cewa, gwamnati za ta tallafa musu.
Talla