Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden a birnin Lima a ranar 16 ga wata, kimanin shekara daya ke nan tun bayan ganawarsu a birnin San Fransisco. Ganawarsu a wannan karo kuma ta kasance ta uku a tsakaninsu a cikin shekaru hudu da suka gabata.
A kimanin tsawon sa’o’i biyu, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi a kan huldar da ke tsakanin kasashensu da ma batutuwan kasa da kasa, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya takaita wasu abubuwa guda bakwai da ya kamata a yi la’akari da su bisa ga bunkasar huldar kasashen biyu cikin shekarun hudu da suka gabata, kuma ya fara ne da ambaton batun samun kyakkyawar fahimtar juna, inda ya yi nuni da cewa, husuma a tsakanin kasashe masu tasowa da manya ba aba ce da za a ce dole sai an yi ta ba a tarihi. Bai kamata a bari sabon yakin cacar-baka ta barke ba kuma babu mai yin nasara a ciki. Neman dakile ci gaban kasar Sin rashin wayewa ne kuma ba abin yarda ba ne kuma hakan zai fadi kasa warwas.
- Kwalara Ta Yi Ajalin Mutane 25 A Sakkwato
- Shugabannin Sin Da Faransa Sun Rubuta Bayanai Domin Wani Bikin Baje Koli Na Musamman
Yadda kasashen biyu ke fahimtar juna, wato su abokan gaba ne ko aminai ne, ya zama tambaya da dole su amsa lokacin da suke hulda da juna. Don haka, a yayin tuntubar juna a tsakanin manyan jami’an kasashen biyu cikin ‘yan shekarun baya, sun sha tattauna batun.
A cikin ‘yan shekarun baya, kasar Sin ta bunkasa da sauri tare da cimma nasarorin a-zo-a-gani, sai dai hakan ya sa kasar Amurka matukar damuwa. Don kiyaye matsayinta na fin karfi a duniya, ta dauki matakai iri- iri na dakile kasar Sin, ciki har da katse huldar tattalin arziki da ita da yayata kalaman wai “Sin barazana ce”, matakan da kuma suka lalata huldar kasashen biyu. Sai dai abin da Amurka ba ta gane ba shi ne, kowace kasa da kuma kowace kabila tana da ‘yancin bunkasa kanta, kuma manufar kasar Sin ta bunkasa kanta ita ce don al’ummarta su ji dadin rayuwarsu, a maimakon a ce tana neman maye gurbin wata. A sa’i daya kuma, ya kamata Amurka ta gane cewa, babu wanda zai iya hana al’ummar kasar Sin ‘yancinsu na tabbatar da ci gaba. Har ila yau, ya kamata Amurka ta gane cewa, zamanin kasar Amurka na nuna fin karfi ya kare, yadda kasashe masu tasowa ke bunkasa da sauri da ma kasancewar bangarori masu ci gaba da dama a duniya ya zama tabbas, don haka yin hadin gwiwar cin moriyar juna ya zama dole.
Tarihi ya sha shaida mana cewa, hadin gwiwar Sin da Amurka zai amfanawa kowacensu ne, a yayin da kuma dukkansu za su yi hasara idan sun yi fada. Musamman ma a yanayin da ake ciki yanzu, moriyar bai daya tsakanin kasashen biyu ta kara karuwa a maimakon raguwa. Ko ta fannonin tattalin arziki da noma da yaki da miyagun kwayoyi da aiwatar da dokoki da kiwon lafiya, ko kuma a gaban kalubale da baki dayan duniyarmu ke fuskanta irinsu sauyin yanayi da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, har ma a lokacin da ake daidaita batutuwan da ke janyo hankalin kasa da kasa, duka ana bukatar Sin da Amurka su yi hadin gwiwa da juna. Don haka kamata ya yi Sin da Amurka su fadada hadin gwiwarsu.
A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, kasancewarsu kasashe manya, ya kamata Sin da Amurka su dauki nauyin da ke wuyansu, su yi la’akari da makomar dan Adam a ko da yaushe, furucin da ya nuna inda ya kamata huldar kasashen biyu ta dosa.
Hakika, a halin yanzu, duniyarmu na fama da tashin hankali da rikice-rikice, kuma dan Adan na fuskantar kalubalen da bai taba gani ba. Huldar da ke tsakanin Sin da Amurka na shafar al’ummominsu, har ma da makomar dan Adam baki daya. Don haka, daukacin kasashen duniya na fatan ganin kasashen biyu su kyautata huldarsu, haka kuma suna fatan ganin ci gaba cikin lumana da hadin gwiwar cin moriyar juna ya zama jigon zamanin da muke ciki. Kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su dauki nauyin da ke bisa wuyansu, su yi la’akari da ci gaban duniya, su samar da tabbas ga duniyar da ke fama da rashin tabbas. (Lubabatu Lei)