Bisa kalubalen da suke fuskanta na gudanar da aikinsu a kullum rana, hukumar gudanarwar kamfanin sufuri da zirga-zirgan Jirgin sama ta Aero ta sanar da dakatar da aikace-aikacenta na kwasan fasinjojinta na wucin gadi da zai fara aiki daga ranar Laraba 20 ga watan Yulin 2022.
Wannan bai shafi hidimar hayar jiragen safara wato AeroMRO, da sashin makarantar horaswa ta Aero (ATO), ayyukan jirage masu saukar ungulu ( Helicopter) ba.
A sanarwar da kamfanin ta fitar a ranar Litinin, na cewa wannan matakin ya zama musu tilas ne su dauka bisa ababen da suke faruwa a zahirance na wahalar kula da ayyukansu kuma hakan ka iya zama basu gamsar da kwastomominsu yadda ya dace ba.
Sanarwar ta ce, nan da ‘yan makwanni masu zuwa za su dawo su cigaba da jigila amma a yanzu haka dole su dakatar domin tabbatar da kula da lafiya walwala da jin dadin abokan huldarsu wadanda da haka ne aka sansu kuma ‘yan kwangilarsu ke kokari a kowani lokaci.
“A ‘yan watannin baya da suka wuce masana’antar jiragen sama na fuskantar kalubale masu tarin yawa kuma hakan ya shafi kamfanonin jiragen sama. Matsalolin da suka hada da tsadar farashin Man tuki, Hauhawarsa da ma karancin samunsa a kasuwannin duniya. Wadannan na daga cikin matsalolin da suke damun kamfanonin sufuri a yanzu”.
Kamfanin ya ce za su cigaba da duba abubuwan da suka dace kuma kwanan nan za su dawo su cigaba da sufuri, “Muna tabbatar wa kwastomominmu da masu ruwa da tsaki cewa kwanan nan za mu dawo kuma kada su ji ko dar na samun jin dadin sufuri daga garemu”.
“Don haka muna bai wa kwastomominmu hakuri bisa wannan duk wani rashin jin dadi bisa wannan matakin muna bada hakuri a kai kuma muna tabbatar musu za mu dawo kwanan nan.”