Kamfanin ‘Nigerian Breweries PLC’ ya yi asarar Naira biliyan 106 a shekarar da ta gabata ta 2023, sabanin ribar Naira biliyan 13.93 da aka samu a shekarar 2022, wanda hakan ke nuna kamfanin ya tabka asarar kashi 860% cikin 100%.
Mista Uaboi Agbebaku, Sakataren Kamfanin, Nigerian Breweries ya bayyana haka a cikin sakamakon tantance kudaden da kamfanin na shekarar 2023 da aka aika zuwa ga Nigerian Exchange Ltd. (NGX).
- Ƙungiyar Ƙwadago Za Ta Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Adawa Da Tsadar Rayuwa
- Zargin Badakala: Emifiele Ya Sake Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Dala Miliyan 6
Agbebaku ya ce ribar da kamfanin ya samu na shekarar da ake bitarta ita ma ta ragu da kashi 0.3 zuwa Naira biliyan 212.5, idan aka kwatanta da Naira biliyan 213.20 da aka fitar a shekarar da ta gabata.
Ya bayyana cewa ribar da kamfanin ke samu ya ragu da kashi 15.3 zuwa biliyan 45, sabanin Naira biliyan 53 da aka samu a shekarar da ta gabata.