Kamfanin Azman Air ya musanta rahoton da ake yadawa na cewa ya sayar wa Iran jiragensa.
An samu rahotonni da ke zargin cewa, Azman ya sayar da jiragensa guda biyu ga Iran ba tare da bin ka’ida ba, kuma ya saba wa takunkumin da kasashen duniya suka kakabawa Iran.
- Bukukuwan Kirismeti: Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Iyalan Waɗanda Suka Rasu Sakamakon Turmutsitsi A Wasu Jihohi
- Wike Ya Bai Wa Asibitocin Gwamnati Umarnin Tallafa Wa Wadanda Turmutsitsin Abuja Ya Rutsa
Jirgin – Airbus A340-600 mai lamba 5N-AAM da Boeing 737-300 mai lamba 5N-YSM – an sayar da su ba tare da sanin hukumar NCAA ba.
Sai dai kamfanin jirgin ya musanta zargin, yana mai cewa, jirginsa ya je Iran ne kawai don kula da lafiyarsa (C-Check).
Babban manajan kamfanin na Azman Air, Muhammad Hadi AbdulManaf, ne ya mayar da martani yi a kan zargin, inda ya ce jiragen nasu sun je Iran ne kawai don kula da lafiyarsu akan tsarin (C-Check) kamar yadda hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya NCAA ta ba da umarni.