Shahararen kamfanin gine-ginen nan a kasar Sin ‘China Harbour Engineering Company (CHEC) Nigeria Limited’ ya bayyana cewa, a halin yanzu ya samu nasarar kammala aikin fadada hanya mai tsawon kilomita 5.4 data taso daga Abuja zuwa Keffi da kuma hanyar da ta taso daga Keffi-Akwanga-Lafia-Makurdi mai stawon kilomita 220.
Kamfanin ya tabbatar da haka, ya kuma ce, a karkashin yarjejeniyar ta samar da cewa, su za su ci gaba da kula ta hanyar har zuwa shekara 25 masu zuwa.
- Ko Tinubu Zai Hakura Da Ganduje Ya Rungumi Kwankwaso?
- Sakamakon Binciken CGTN Ya Karkata Ga Goyon Bayan Tsagaita Wuta Da Kawo Karshen Yaki Tsakanin Falasdinu Da Isra’ila
A rangadin da shugaban kamfanin, Wang Jujin ya yi da ‘yan jarida, ya ce kasar Sin ta bayar da tallafi mai yawa a hakar gudanar da aikin ta hanyar samar da gadoji da kuma hanyoyin jigin kasa a sassan Afrika da dama.
Wadannan ayyukan da muka gudanar sun taimaka wajen farfado da tattalin arzikin al’umma da dama a yankin Afrika. Wannan kuma na daga cikin akidojin kasar Sin na gina al’umma tare da tabbatar da bunkasar al’umma gaba daya.
Ya kuma bayyana cewa, ayyukan gyaran hanya da kamfanin ya yi a yankin Nijeriya ta tsakiya ya taimakwa wajen farfado da zirga-zirgan al’umma da tattalin arzikinsu.