Kamfanin gudanar da ayyukan Injiniya na kasar Sin, watau CHEC, a ranar Juma’ar nan ya mika kashi na biyu na tashar ruwa mai zurfi ta Kribi ga mahukunta a kudancin Kamaru.
Da yake jawabi a wajen bikin mika tashar, babban manajan hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Kribi, watau PAK, Patrice Melom, ya ce kammala kashi na biyu na tashar zai kara habaka aikace-aikacenta.
A yayin da yake yaba wa kamfanin CHEC bisa kyakkyawan hadin gwiwa da gudanar da komai cikin sauki, Melom ya kara da cewa, tashar jiragen ruwa ta PAK ta kasaita a halin yanzu. Domin a kashinta na farko, zurfinta bai wuce mita 615 ba kawai. Yanzu kuma ta kara samun ci gaba zuwa mita 715, inda hakan zai ba da damar samun karin zirga-zirga a tashar jiragen ruwan.
A shekarar 2018, CHEC ya kammala kashin farko na tashar jiragen ruwan, wadda ta kara wa tattalin arzikin kasar ta Kamaru tagomashi. Kana a shekarar 2019 ne kuma aka fara aikin kashi na biyu na tashar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)