Microsoft, kamfanin fasaha ta kasar Amurka, ya kori ma’aikatansa da ke aiki a cibiyar bunkasa Afrika (ADC) da ke jihar Legas a Nijeriya.
 Cibiyar ADC na daga cikin ressan kamfanin Microsoft a Afrika da ke aikin injiniyanci wajen nemo mafita da habaka ci gaba na duniya gami da samar da guraben ayyuka hadi uwa uba da bunkasa fasahar zamani ta hanyar kere-kere a nahiyar.
- Sabon Shirin Auren Zawarawan Kano A Sikeli
- Abubuwa Uku Da Za A Yi Farashin Kaya Ya Sauka A Nijeriya – Dakta Saleh
 Da yake tabbatar da lamarin a ranar Laraba, wani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa majiyarmu cewa an kori ma’aikatan ne bisa wani dalilin da har yanzu ba a sani ba.
 An kuma labarto cewa kamfanin ya ma rufe ofishin na ADC da ke Legas.
 Wannan lamarin dai na zuwa ne bayan shekara hudu da kamfanin Microsoft ya bude aikace-aikacensa a Nijeriya.
A watan Mayun 2019, kamfanin Microsoft ya sanar da bude ofishin bunkasa nahiyar Afrika a Nijeriya da Kenya, wanda ke da manufar bunkasa kere-kere da fasahar zamani ba kawai a nahiyar Afrika ba har ma da duniya baki daya.
Kamfanin Microsoft dai ya kasance na kira ga injiniyoyi da su yi amfani da basirar kirkirarriya ta (AI) da na’urorin koyi.
 Kamfanin dai ya dukufa wajen zuba dala miliyan 100 a cikin ayyukansa na farkon shekaru biyar.
 A ranar 21 ga watan Maris na 2022 ne aka bude ofishin kamfanin da ke Legas. Ofishin dai ya maida hankali wajen kenkeshe kwararrun injiniyoyi da bunkasa tsarin bunkasa tattalin arziki ta hanyar amfani da fasaha gami da kyautata bangaren kere-kere.