Ba wai ruwa ne kawai a cikin kwalba ba, ya samu amincewa a kowane ɓangare.
Tsarinsa Saboda Tsaro Da Ɗorewarsa
Kamfanin Nestlé Pure Life ya samar da tsaftaccen ruwan sha ga ‘yan Nijeriya sama da miliyan 100. Saboda tsabtarsa da ingancinsa ya sa Jaridan LEADERSHIP ya karrama shi da kyautar gwarzon kamfani da ke samar da kaya ta shekarar 2025.
Kamfanin Nestlé Water Pure Life Nigeria Plc, yana sarrafa kayan gida da ya kasance mai bayar da cikken ɗalafiya.
Daga rijiyoyin ƙarƙashin ƙasa masu kariya zuwa tsabtace ruwa a matakai da dama, tacewar carbon, da kashe kwayoyin cuta ta ultraɓiolet, kowace kwalba na ɗauke da tabbacin inganci wanda miliyoyin iyala daga Nijeriya ke samun aminci a duk kullum.
- Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
- Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul
Inganci Mai Tsafta Da Ƙirƙira Mai Ɗorewa
Ƙarfin kamfanin Nestlé Pure Life yana cikin daidaiton tsarinsa da kuma manufar da ke bayansa.
Kamfanin yana ƙara ingancin ma’adinai cikin ruwan da aka tsarkake domin ɗanɗano da lafiya, yayin da yake jagorantar ƙirƙire-ƙirƙiren ƙunshin kayan muhalli masu aminci waɗanda ke sake fasalta ma’aunin masana’antu.
An gabatar da murfin da za a iya sake sarrafawa masu bayyana a shekarar 2025 wanda ke ƙara yiwuwar sake sarrafa kwalaben.
Kashi 50 cikin ɗari na PET da aka sake amfani da shi yanzu ana amfani da shi a dukkan ƙunshin kayanta.
An samu raguwar kashi 15 cikin ɗari na amfani da filastik tun daga shekarar 2013 ta hanyar fasahar kwalban mai inganci.
Waɗannan sauye-sauye, ko da yake na fasaha, suna tafiya da harshen duniya na tabbatar da jin daɗi ga masu amfani a yau ba tare da rage albarkatu na gobe ba.
Dubarun Ɗorewa
Bayan samar da kayayyaki, kamfanin Nestlé Nigeriya ya sake samun dubarun ɗorewa a cikin ayyukansa.
A masana’antar ƙera kayayyaki ta zamani da ke Abaji, tana da inganci da kula da muhalli, tana rage amfani da ruwa, rage sharar gida, da samar da ƙarin ayyukan yi a cikin gida.
Aikin da kamfanin ke ci gaba da yi na samun takardar shaidar haɗin gwiwar gudanar da ruwa (AWS), yana ƙarfafa alƙawurinsa na kiyaye tsarin ruwa na Nijeriya ta hanyar ɗorewa, inganci, da gaskiyar shugabanci.
A watan Agusta 2025, Nestlé Nigeria ya ƙaddamar da kamfen na kasa don wayar da kan jama’a kan ingancin ruwa tare da haɗin gwiwar OPS-WASH, yana jaddada cewa ‘yan Nijeriya miliyan 113 har yanzu ba sa iya samun tsaftataccen ruwan sha.
Shirin, wanda aka yayata ta hanyar kafofin watsa labarai, ya koyar da gidaje yadda za su kare kansu da rage gurbatan muhalli da rungumar dabi’un amfani da tsaftataccen ruwan sha.
Wannan wani kamfen ne da aka gina bisa jin ƙai, kuma an ƙarfafa shi da hujjoji, yayin da Nijeriya ke rasa kusan naira biliyan 455 a shekara sakamakon illolin rashin tsaftataccen ruwa da rashin tsaftar muhalli.
Tushen Gwazo Kan Manufa
Duk da ci gaba da fafutuka, kasuwancin ya kasance mai wahala. A rabin farko na shekarar 2025, Nestlé Nigeria ya samu kuɗaɗen shiga na naira biliyan 581.1, ƙaruwar kashi 43 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, da riba kafin haraji na nair biliyan 88.4, bayan ya fuskanci asara na naira biliyan 252.5 a shekarar 2024.
Waɗannan sakamakon sun nuna nasara guda biyu: juriya ta kuɗi da tasirin zamantakewa a ɓangaren hangen nesa guda na kamfanin.
kamfanin Nestlé Pure Life yana ci gaba da faɗaɗawa tare da nau’ikan ruwa mai inganci da ruwan lemun, wanda aka ƙunsa cikin wani mazubi na roba.
Kowane sabon ƙirƙira yana nuna falsafar, ruwa mai tsabta da inganci.
Ilmantarwa Bayan Masana’anta
Kamfani Nestlé, yana wayar da kan al’umma tare da ilmantar da su. Ta hanyar shirinsa na “Ranar Ilmantar Ruwa”, ɗaliban makaranta a faɗin Nijeriya suna koyon kimiyya da nauyin tsaftar ruwa.
Ta hanyar koyar da matasa masu tasowa, kamfanin yana tabbatar da cewa ɗorewa ba kawai darajar kamfani ba ce har ma da ta al’umma.











