Kamfanin mai na kasa (NNPCL), ya bayyana a ranar Laraba cewa, ya zuwa watan Oktoba na wannan shekarar, ya zuba Naira Tiriliyan 4.5 a asusun tarayya.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da ya gana da kwamitin kudi na majalisar dattawa.
- NNPCL Ya Gargadi Masu Ɓoye Fetur Don Tsoron Ƙarin Farashin Man Da Samun Ƙarancinsa
- Ina Tattalin Arzikin Sin Ya Dosa? Babban Taron Aikin Raya Tattalin Arziki Ya Ba Da Amsa
A cewarsa, yayin da dokar masana’antar man fetur ta fara aiki, kamfanin NNPCL ya kasance babban jigo a kasuwar mai da iskar gas ta duniya.
“Ina mai farin cikin sanar da ku – Shugaban kwamitin kudi na Majalisar Dattawa da sauran ‘yan kwamitin cewa, ya zuwa watan Oktoba, mun zuba Naira Tiriliyan 4.5 a asusun tarayya a matsayinmu na kamfanin kasar nan a shekarar 2023.” Inji Kyari