Kamfanin samar da kayan dandano na Onga daga Promasidor Nigeria, sun yi bikin cika shekaru 10 da kaddamar da dunkulen Onga a babban ofishin kamfanin tare da kaddamar da garabasar “Onga Taste the Millions”, wanda aka tsara don inganta dandano ga rayuwar masu amfani da su.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a babban ofishin kamfanin, tawagar Onga ta gabatar da wata garabasa, inda kamfanin ya yi alkawarin bai wa masu amfani da kayansa makudan kudade da kuma kyautuka na da kuxinsu ya kai Naira miliyan 250.
- A Shirye Sin Take Ta Tsara Yarjeniyoyin Ciniki Cikin ’Yanci Da Karin Kasashe Masu Tasowa
- An Tabka Asarar Miliyoyin Kuɗaɗe A Gobarar Kasuwar Wayoyin Salula Ta Jihar Kogi
Ma’aikata, wakilai daga kafofin yada labarai na cike da farin ciki a wurin taron lokacin da ake kaddamar da garabasar.
Za a fara gudanar da wannan dinbin garabasa ta “Onga Taste the Millions” daga 1 ga Satumba zuwa 31 ga Oktobar 2024, inda za ba da kyaututtuka da yawa masu kyau gami da yawa a kyaututtuka na mako-mako.
Mutum 10 da suka yi nasara za a basu Naira 1,000,000 a kowane mako, tsawon makonni 8, sai kuma mutum 5 da suka yi nasara suma za su samu kyautar Naira 500,000 na tsawon makonni 8, sannan wasu mutum 10 da suka yi nasara za su samu kyautar Naira 100,000 a duk sati har tsawon makonni 8, mutum 40 kuma da suka yi nasara za su samu kyautar Naira 50,000 a duk mako tsawon makonni 8. Sai kuma mutum 325 da suka yi nasara za su gajiyar Naira 10,000 duk mako na tsawon makonni 8, mutum 1,800 da suka yi nasara za su samun garabasar Blender da Tukunyar gas sannan sama da mutum 200,000 za su ci gajiyar kyautar katin buga waya nan take.
Da yake tunatar da tsawon shekaru da Onga Bouillon cube ya yi, Babban Jami’in Gudanarwa, Francois Gillet, ya bayyana cewa nasarar da kamfanin ya samu a tsawon shekaru shaida ce ga ci gaba da habaka samfura masu inganci.
Ya kuma bayyana muhimmancin wannan biki, inda ya ce, “Nasarar Onga a cikin shekaru goma da suka gabata, wata alama ce da ke nuna amincewar masu amfani da kayanmu.
Ta hanyar tallata ‘Onga Taste the Miliyoyin’, muna farin cikin bayar da gudummawa ga al’ummarmu ta hanyar ba da kyauta ga masu saye sama da 250,000 waxanda suka taka rawa wajen sanya Onga ya zama abin alfahari ga magidanta.
Wannan biki ba wai an yi shi ne saboda abubuwan da suka gabata ba, a a har ma da sadaukarwa domin na gaba.
A cewar Daraktar Kasuwanci, Adebola Williams “Mun yi farin ciki da kaddamar da wannan garabasa, wacce ita ce hanyarmu ta nuna godiya ga abokan cinikinmu masu aminci don ci gaba da samun goyon baya.”
Ta kuma nuna jin dadi game da wannan garabasa. “Muna da kwarin gwiwar cewa za ta kasance babbar nasara, kuma za ta taimaka wajen tabbatar da Onga a matsayin jagorar kayan abinci a Nijeriya,” in ji ta.
Oladapo Oshuntoye, Manajan Rukunin Abinci na Promasidor Nigeria, ya bayyana farin cikinsa game da wannan shiri, yana mai cewa, “Wannan bikin ba wai kawai don murnar nasarorin Onga ya samu ba ne, har ma da sanin masu amfani da su wadanda suka sa nasararmu ta samu a yau.
An tsara garabasar ‘Onga Taste the Miliyoyin’ don sanya farin ciki da kuma lada ga dubban magidanta, tare da karfafawa Onga a cikin kayan dandano da zabi ga al’aummar Nijeriya.
Haka kuma taron ya samu halartar wasu manyan masu ruwa da tsaki kamar Hukumar Kula da Gasa da kare hakkin masu amfani da kaya ta Tarayya (FCCPC), da Hukumar Lotteries da Gaming ta Jihar Legas (LSLGA).