Manchester City ta tsawaita yarjejeniyar samar da kayan wasanta da babban kamfanin samar da kaya na Puma na tsawon shekaru 10, sabuwar yarjejeniyar zai sa City ta samu zunzurutun kuDi har fan biliyan 1, hakan ya sa ta zama yarjejeniyar samar da kayan wasa mafi girma a tsakanin kungiyoyin dake buga gasar Firimiya, da farko City ta sanya hannu kan yarjejeniyar fan miliyan 65 a shekara tare da kamfanin dake kasar Jamus a shekarar 2019, amma bangarorin sun amince da tsawaita wa’adin zuwa shekarar 2035.
Manchester City ta dauki kofi uku rigis a shekaru biyu da suka wuce amma ta kare kakar da ta gabata ba tare da wani babban kofi ba, wannan yarjejeniyar da City ta kulla da Puma ta zarce yarjejeniyar fan miliyan 90 da abokan hamayyarta Manchester United suka kulla da kamfanin Adidas a shekarar 2023.
City ta samu manyan nasarori tsakanin shekarar 2019 zuwa 2024 inda ta lashe kofi 4 na gasar Firimiya Lig tare da daukar kofuna 3 rigis shekaru biyu da suka gabata, amma ta kare kakar wasan da ta gabata ba tare da wani babban kofi ba, City ta bayyana fan miliyan 715 a matsayin kudin shigar da ta samu a shekarar 2024, yayin da kudin kasuwancinta ya karu da fan miliyan 344, wanda babu wata kungiya a Ingila da ta taba samun irin wannan kudaden a shekara 1.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta City, Ferran Soriano ya ce “Mun hada karfi da karfe tare da Puma domin samar mana da kayan wasanni da suka hada da riga da wando, takalma, kwallon atisaye, rigar atisaye da sauran kayan wasanni na bukata, Puma ta kasance kamar gida a wajenmu domin mun dade a tare ba tare da wata matsala ba”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp