Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya.
Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada hannu don haifar da moriyar juna da cimma nasara tare, ta yadda tattalin arziki, da zamantakewar wurin za su iya samun ci gaba mai kyau.
A nasa bangare, Dai ya ce, shirin da kamfaninsa ya ba da taimakon gudanarwa, ya shaida kwarewar kamfanin a bangaren shimfida layin dogo, kuma alama ce ta hadin gwiwar kasashen biyu. Kazalika, CRCC zai ci gaba da hadin gwiwa da Aljeriya a bangaren zirga-zirga, da makamashi, da sabbin sana’o’i da sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp