An gudanar da bikin kaddamar da ginin katafaren wurin yawon shakatawa na zamani da kamfanin kasar Sin na Greenhouse International Development Group zai yi a Afienya dake kusa da birnin Tema mai tashar jiragen ruwa, a kasar Ghana.
Bayan an kammaluwarsa, ana sa ran wurin yawon shakatawar ya kunshi babban otel mai taurari 5 wato five-star mai dakuna 160 da wasu dakunan alfarma masu zaman kansu guda 20, da babban dakin taro da nune-nune da zai iya karbar taron kasa da kasa mai mutane 5,000 da yankin ruwa mai girman muraba’in mita 160,000 da kirkirarren bakin teku da wuraren wasan kwallon Golf da dakin cin abinci a bakin ruwa da jiragen ruwa.
Shugaban Ghana John Dramani Mahama wanda ya aza harsashin ginin, ya yaba wa masu zuba jari na kasar Sin bisa kwarin gwiwar da suke ci gaba da nuna wa kan kasar a matsayin wurin zuba jari.
Shugaba Mahama ya kuma yabawa kamfanin Greenhouse International Development Group saboda irin ayyukan da ya gudanar a kasar tun daga shekarar 2011 da ya shiga Ghana, ciki har da yankin masana’antu na Bright International Industrial Park da masana’antu da dama masu samar da kayayyaki a farashi mai rahusa ga ‘yan kasar da samar da gurabun ayyuka kimanin 10,000 tare da zuba jari a bangaren aikin gona da na gine-gine. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp