A jiya Juma’a ne kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Habasha ko EEU da kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, domin samar da wutar lantarki ga jama’ar da ke zaune a yankunan da ba su da wutar lantarki a kasar Habasha.
Yarjejeniyar, wadda aka rattaba hannu a kai a taron kolin makamashi mai tsafta na kasar Habasha na shekarar 2024 a Addis Ababa, babban birnin kasasr, wani bangare ne na aikin samar da wutar lantarki na kasa da ke da nufin cimma nasarar samar da wutar lantarki a daukacin kasar ta gabashin Afirka nan da shekarar 2030, a cewar Shiferaw Telila, babban jami’in gudanarwa na kamfanin EEU. (Mai fassara: Yahaya)