Bankin bunkasa aikin noma da ke Nahiyar Afirka (ADB), ya rattaba hannun yarjejeniyar bayar da bashin dala miliyan 75 tsakaninsa da kamfanin sarrafa takin zamani na Indorama da kuma kamfanin samar da sinadarin sarrafa taki na ‘Chemicals Limited’.
Wannan bashi, zai bai wa kamfanin Indorama damar sarrafa takin da za a fitar zuwa kasashen waje tare da kara samar da wadataccen abinci da kuma bunkasa kasuwa ta kasa da kasa da kara samar da ayyukan yi a fadin wannan kasa.
- Firaministan Kasar Sin: Bikin Baje Koli Na Canton Fair Zai Ci Gaba Da Haskakawa A Sabon Zamani
- Ministocin Tsaro Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawa Ta Kafar Bidiyo
Har ila yau, kara fadada wannan aiki ya hada da bunkasa takin zamani nau’in urea da kuma gyaran sabbin kayan aikin sarrafa takin zamani na kamfanin Indorama da ke garin Fatakwal.
Kazalika, ana sa ran za a samar da tan miliyan 1.4 na nau’in takin; inda kuma karin aikin sarrafa wannan taki na urea daidai har guda biyu na Indorama, zai wadaci manoma a Nijeriya da kuma wanda ake sa ran fita da shi zuwa kasuwar duniya.
Mukaddashin Darakta na Masana’antar Bunkasa Kasuwanci a sashen na Bankin Ousmane Fall ya bayyana cewa, bankin na tunkaho da hadakar da ya yi da kamfanin takin Indorama, IFC da sauran makamantansu a cikin wannan aiki.