Twitter ya mayar da martani ga sabuwar sabuwar manhajar sada zumunta ta zamani mai suna Threads, ta kamfanin Meta a ranar Alhamis, inda ta yi barazanar kai karar kamfanin.
A cewar wani rahoto da Semafor ya fitar, ya bayyana cewa an aikewa, Mark Zuckerberg, wasika kamar yadda wani lauyan Twitter, ya ce, kamfanin ya yi matukar damuwa da kutsen fasaha da Meta ya yi da gangan da kuma satar sirrin yadda tsarin kasuwancin Twitter yake.
Alex Spiro ya rubuta a cikin wasikar “Twitter yana da haƙƙin mallakar fasaha, kuma yana buÆ™atar Meta ya É—auki matakan gaggawa don dakatar da amfani da duk wani sirrin kasuwanci na Twitter ko wasu bayanan sirri.”
Wakilan Twitter da Meta har yanzu ba su ce uffan ba game da karar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Meta ya kaddamar da sabuwar manhajar sadarwa kishiyar Twitter a kasashe 100. Sabuwar manhajar ta samu rajistar sama da mutum miliyan 30 kasa da awanni 24 bayan kaddamar da ita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp