A wata sanarwa da Hukumar Jiragen Kasan Nijeriya (NRC) ta fitar, ta bayyana cewa, kamfanoni fiye da 530 suka nuna aniyarsu na aikin gyare-gyare na kayyakin hukumar jiragen kasa na Nijeriya a wannan shekarar 2024.
An dai ware za a kashe naira Biliyan 11 ne a wanann shekarar don aiwatar da ayyukan da suka shafi bunkasa harkokin jiragen kasa a Nijeriya da suka hada da samar bda hanyar jirgin da taragu da sauran kayyakin aikin da ake bukata don bunkasa harkokin sufurin jiragen kasan Nijeriya a wannan shekarar kamar yadda aka sanya a cikin kasafin kudin 2024.
- Kotu Ta Ci Tarar ‘Yansanda Naira Miliyan 300 Kan Kisan ‘Yan Shi’a A Zariya
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron OIC Karo Na 15
An bude zama tantace kamfanonin ne a shalkwatar Hukumar Jiragen Kasan Nijeriya da ke Legas, inda shugaban Hukumar, Engr Fidet Okhiria, ya jagoranci zaman, ya kuma nuna muhimmancin ba kowa hakkin nuna bajintarsa na aiwatar da aikin da ake bukata.
Ya kuma jaddada cewa, za a gudanar da tantancewar cikin gaskiya da amana, ta yadda kowa zai gamsu da sakamakon da za a fitar.
Darakta mai kula da ma’aikata a hukumar, Dr. Monsurat Omotayo, ta wakilci shugaban hukumar ta kuma bayyana makasudin taron kamar haka “Wannan wani shiri ne da muke gudanarwa a duk shedkara. Hukumar mu ta tallata ayyukan da ake bukatar kamfanonin da suke da kwarewar yin aikin su mika bukatarsu tun a watan da ya wuce, a kan haka muka taru a yau don tantance wadanda suka kware na yin aikin da ya kamata a shekarar 2024.”
Ta kuma jaddada cewa, “Wannan bikin zai taimaka mana gudanar da tantancewar a cikin adalci ta yadda kowa da kowa zai gamsu da abin da aka yi, hakan kuma ya yi daidai da dokar bayar da ayyukan kwangila a Nijeriya.”
Ganin yadda kamfanoni da dama kuma daga bangarori da dama suka nuna bukatarsu, ya zama dole mu yi aiki cikin natsuwa don fitar da kamfanin da ke da kwarewar da ake bukata don aiwatar da ayyukan da ke gabamu” in ji ta.