Alkaluma daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin sun nuna cewa, kudin shigar kamfanoni mallakin gwamnatin Sin ya karu da kaso 1.3 a shekarar 2024.
A cewar ma’aikatar, kamfanonin sun samu karuwar yuan triliyan 84.72, kwatankwacin dala triliyan 11.7 na kudin shiga a 2024.
Jimilar ribar da suka samu a shekarar 2024 kuma, ta karu da kaso 0.4 zuwa triliyan 4.35 a kan na shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp