Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta ce kamfanoni mallakin gwamnatin kasar, sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata cikin watanni hudu na farkon shekarar nan ta 2025, inda jimillar kudaden shigarsu ta ci gaba da karuwa bisa daidaito a shekara guda.
Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, sun nuna tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu, jimillar kudaden gudanarwa na wadannan kamfanoni ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 26.276, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.65, adadin da ya nuna daidaito matuka idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2024. (Mai fassara: Saminu Alhassan)