Alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samar a kwanakin baya sun shaida cewa, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin samar da rangwamen gwamnati ta musayar sabbin motoci da tsofaffi, yawan bukatun da aka mika na yin musayar tuni ya wuce miliyan 10, matakin da ya yi matukar rage kudin da masu sayayya suka biya, baya ga kuma karuwar motocin da kamfanonin sai da motoci na gida da waje suka sayar.
Lamarin hakan yake ma ga kasuwar sai da Kayayyakin laturoni na amfanin yau da kullum a gidaje. In mun dauki misali da dandalin sai da kayayyaki na Suning.com, tun bayan da aka fara aiwatar da tsarin samar da rangwamen gwamnati ta musayar sabbin kayayyaki da tsofaffi a watan Satumban bara, yawan kayayyakin laturoni na amfanin yau da kullum a gidaje masu tamburan gamayyar jarin Sin da waje da aka sayar ya karu da kaso 44.7%. Wato ke nan kamfanoni masu jarin waje ma sun amfana da tsarin nan da aka aiwatar.
- Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?
- Dan Asalin Jihar Kano Ya Kafa Tarihin Kirkirar Manhaja Mai Auna Tsayin Bishiya A Faransa
Ma iya cewa tallafin da aka samar ta fannin manufofi da ma kwaskwarima da aka yi wa kasuwannin kasar Sin, ya samar da babbar dama ga kamfanoni masu jarin waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp