An yi taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka tambaya cewa, kwanan baya, kungiyar kasuwanni na Sin da Jamus da na Sin da Austriliya sun jin ra’ayin kamfanoninsu dake nan kasar Sin, yawancinsu suna amince da kuzarin kasuwannin kasar Sin da ma fatan ci gaba da zuba jari a kasar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana matsayin da Sin ta dauka kan wannan batu.
Ya ce, Sin ta karanta rahoton da aka bayar na cewa, kamfanonin Jamus a Sin da yawansa ya kai kashi 77% suna ganin cewa, za su samun karuwar riba a nan kasar Sin a cikin shekaru 5 masu zuwa, yayin da kashi 66% na kamfanonin Austriliya dake Sin suna shirin habaka zuba jari a Sin, kuma na kashi 58% suna mai da kasar Sin daya daga wurare 3 dake kan gaba a duniya a bangaren zuba jari.
Abin da ya bayyana kwarin gwiwar al’ummar duniya game da makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, Sin za ta zama wuri mafi jawo hankali masu zuba jari ciki hadda kamfanonin Jamus da Austriliya.(Amina Xu)