A halin yanzu gwamnatin Jihar Edo ta bayar da lasisi ga kamfanoni masu hakar ma’adanai 40 don su ci gaba da harkokin haka da sarrafa ma’adanai a fadin jihar.
Kwamishinan ma’adaia na jihar, Enaholo Ojiefoh, ya bayyana haka a tattunawarsa da manema labarai a garin Benin babbar birnin jihar ranar Litinin, ya ce, jihar ta yukuro ne ta nemo tare da raba lasisin don kada a barta a baya wajen cin gajiyar ma’adanai da Allah ya shimfida a fadin jihar, ya kuma ce wannan mataki zai taimaka wa jihar shiga tsarin jihohi masu bunkasar tattalin arziki wanda zai kuma taimaka wa matasa samun aikin yi da rage zaman kashe wando.
- Gwamnan Bauchi Ya Biya Kashi 50 Na Karin Kudin Kujera Ga Alhazan 1652
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Benin Domin Tattauna Hanyoyin Karfafa Dangantakar Kasashensu
Ya kuma lura da cewa, za a tabbatar da kamfanonin da za su amfana kamfanoni ne da suke da ra’ayi tare da shirin shiga don a dama da su a bangaren ma’adanai na jihar.
Ya kuma bayyana cewa, “Da lasisin ya shiga hannun mu mun kai ziyara wuraren da ake da wadannan ma’adanai don tattaunaws da al’ummar da ke wurin. A kan haka kuma mun samu masu sha’awa daga kasashen waje da dama daga watan Janairu zuwa Disamba wadanda suke shirye na shigowa da kudadensu don aikin hakar ma’adanai a kasar nan.
“Domin cin cikakkiyar gajiyar wannan lamarin, gwamnan jihar ya umarci a samar da dukkan abubuwan da ake bukata na samun nasara, a kan haka an bude ofis a garin Dangbala da ke karamar hukumar Akoko Edo don zama matattarar bayanai da za a yi amfani da su wajen shirya yadda za a tunkari lamarin.
“Muna da manyan Farfesoshi daga jami’o’i da muke aiki tare muna kuma da ma’aikata a sassa daban-daban da suke taimakawa don samun nasarar da ake bukata.”
Amishinan ya ce, jihar Edo na da dinbin ma’adanai da suka hada da kaolin a garin Ubiaja, da kuma gypsum a yankin Warrake.