Jaridar leadership ta gano cewa kamfanoni 54 suka kasa ko kuma suka ki biyan kudaden ribar da ake rarrabawa ga masu hannun jari a karshen shekara tun shekara 5 da suka wuce.
A duk karshen shekara kamfanoni kan raba wa masu hannun jari ribar da aka samu a cikin shekarar. Amma bayani ya nuna cewa, daga cikin kamfanoni 153 da suke da rajista a kasar nan 54 daga cikin su ba su biya irin wannan kudaden ba ga masu hannun jarinsu tun shekarar 2019, wanda hadakar kudaden ya zama jarin da kamfanion ke tafiyar da harkokinsa da su, wannan yana nuna cewa kashi 34 kenan na kamfanonin da ke Nijeriya suka ki biyan wannan kudaden ga masu zuba jarin su.
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
Masana sun bayyana cewa, rashin biyan riba ga masu zuba jari ba wai yana nufin kamfani baya samun riba ba ne ko kuma bai kamata a zuba jari a kamfanin ba ne amma ya dangantane da irin tsarin da kamfanin yake da shi na yadda zai rika rarraba ribar da aka samu a kasrshen shekara.
Wasu kamfanonin sun gwamnace su sake zuba jari da ribar da suka samu don fadada kamfani wasu kuma sun ci karo da asara ko kuma rashin samun riba saboda karyewar tattalin arziki kasa a kan haka suka dakatar da raba wa masu jari ribar da aka samu don ci gaba da wanzuwar kamfanin.
Kididdiga daga hukumar kula da kamfanonin Nijeriya ya nuna cewa, kamfanoni hudu sun bayar da riba ga masu zuba jari a shekara 5 da suka wuce, kamfanoni uku sun bayar a shekara 6 da suka wuce, kamfani 2 sun bayar da ribar a shekara 7 da suka wuce yayin da kamfani 2 suka biya irin wannan kudin shekara 7 da suka wuce; haka kuma wasu kamfanoni 2 sun biya ribar na karshe ne a shekara 8 da suka wuce, kamfani 2 kuma sun bayar da kudin riba ne shekara 11 da suka wuce.
Bayanin ya kuma nuna cewa, kamfani 3 sun biya kudaden ne na karshe shekara 13 da suka wuce yayin kamfani 6 suka biya a shekara 14 da suka gabata; wani kamfani ya biya kudin na karshe ne shekara 15 da 16 da suka gabata yayin wasu kamfanioni 3 suka biya a shekara 21 da suka gabata.
Haka kuma kamfanoni kamar ASeM board, Capital Oil sun bayar da ribar na karshe ne a shekarar 2001, ita kuwa kamfanin Rak Unity Petroleum a shekarar 2019 ta bayar da na karshe.
A karkashin kamfanonin harkar gona, kamfanonin FTN Cocoa Processors (ta bayar a shekarar 2010), John Holts (2005) SCOA Nigeria (2015), Arbico Plc, (1998).
Bayani ya kuma nuna yadda wasu kamfanonin suka bayar da ribar hannun jarinsu na karshe kamar haka DN Tyre & Rubber (2002), Champion Breweries (1986), Golden Guinea Breweries (1997), Multi-Tred Integrated Foods (2010), Union Dicon Salt (2002), da kuma Nigerian Enamelware (2016).
A bangaren harkokin bankuna kuma bincike ya nuna cewa sun biya kudaden hannun jari na karshe kamar haka, Unity Bank (2011) Guinea Insurance (2010), Mutual Benefits Assurance (2018), Niger Insurance, Prestige Assurance, Regency Assurance (2019), Sobereign Trust Insurance (2011), Staco Insurance (2008), Standard Alliance Insurance (2009), Unibersal Insurance, Beritas Kapital Assurance (2017), Coronation Insurance (2016).
A kan haka masana suka bayar da shawara cewa, kafin mai zuba jari ya antaya kudadensa a cikin kamfani ya kamata ya binciki tarihin kamfani na biyan masu hannun jari don kada ya yi zaben tumun dare.
Sun kuma lura da cewa, wasu kamfanonin da gangan suke kin raba ribar da aka samu ba wai don rashin kudi ba.
“Sai kaga kamfanoni na hankoron kara fadada harkokin su amma sun ki biyan riba ga masu hannun jari a kamfanin wanda haka yana karya gwiwar masu zuba jari na ciki da kasashen waje, iin ji wani masani da ya bukaci mu sakaya sunansa.