Manajan Darakta na Kamfanin Siminti na Dangote, Arbind Pathak ya bayyana cewa, kamfanonin siminti na duniya ke da alhakin samar da kashi 7 na sinadarin da ke taimakawa wajen haifar da dumamar yanayi a duniya.
Ya bayyana haka ne a taron kamfanonin siminti na Afirika karo na 12 da aka yi a Abidjan ta kasar Cote d’Iboire, kwanan nan.
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
- Muna Rokon Shugaba Tinubu Ya Hana Ministoci Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje – Akpabio
Ya kara da cewa, “Kamfanonin siminti da ke zama muhimmin kayan hadin yin gine-gine a fadin Afirka suna fitar da kashi 7 na sinadarin CO2 a yayin da ake aikin hadawa tun daga yadda ake sarrafawa har zuwa kai wa ga masu amfani da shi.
Ya kuma ce, a halin yanzu kamfanin Dagote yana jagorantar sauran kamfanonin siminti a Afirka wajen rage fitar da sinadarin CO2 ta hanyar amfani da kimiyyar zamani na amfani da wasu sinadaran da basu cutar da muhalli, ya kuma sanya jari don ci gaba da binciken hanyoyin da za a tabbatar da hakan.
Shugaban kamfanin Dangote ya samu wakilicin babban jami’in kamfanin mai suna Dakta Igazeuma Okoroba, ya ce, a halin yanzu suna amfani da wasu hanyoyin samun wutar lantarki ta hanyar amfani da tsirar wanda an tabbatar da cewa suna fitar da karancin sinadarin CO2, wanda hakan zai taimaka wajen rage sinadarin CO2 da kamfanonin ke fitarwa.
Ya lura da cewa, yadda aka yi amfani da tan biliyan 4.2 na siminti a shekarar 2020, an kuma yi hasashen al’ummar duniya zai karu da kashi 12 23 daga na zuwa shekarar 2050 saboda bunkasar birane, bukatar siminti zai kara karuwa.
A kan haka ya nemi masu kamfanonin siminti su fuskanci neman makwafin man fetur wajen ayyukansu don rage fitar da sinadarin da ke cutar da muhalli.