Tawaga ta farko ta ‘yan kasuwan Sin mai kai ziyara ketare da kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya kafa a sabon shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da muke ciki, ta kai ziyara Kazakhstan, don gaggauta mu’amala tsakanin kamfanonin kasashen biyu da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa. Kuma, kamfanonin kasashen biyu sun samu sabon ci gaba a bangaren makamashin gas da man fetur.
Tawagar ta yi tattaunawa mai zurfi da asusun kasar Kazakhstan na Samruk Kayzana da kungiyar ‘yan kasuwar kasar ta Atamekeh a Astana hedkwatar kasar Kazakhstan, tare da gudanar da taron tattaunawa kan tattalin arziki da ciniki tsakanin ‘yan kasuwar kasashen biyu da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa 8, wadanda ke shafar bangaren makamashin gas da man fetur da aikin noma da jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa da sauransu.(Amina Xu)