Kafofin yada labarai da manazarta na kasa da kasa, sun jinjinawa babban taron ‘yan kasuwan kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da aka gudanar ranar Litinin, inda suka ce gwamnatin Sin na marawa wadannan kamfanonin baya wajen taka rawar gani a bangaren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, kuma Sin ta gabatar da sako mai yakini na karawa wadannan kamfanoni kwarin gwiwar bunkasuwa.
A wannan taro dai, ba nanata niyyar nacewa ga manufofi masu tushe da ake bi wajen raya kamfanoni masu zaman kansu a nan kasar Sin kadai aka yi ba, an kuma gabatar da alkiblar samun ingantattun ci gaba yadda ya kamata a wannan bangare. Hakan ya sa, “kwarin gwiwa” ta sake zama muhimmiyar kalma ga kasashen waje don leka bunkasuwar kasar Sin.
A shekarar da ta gabata, yawan kudin shige da fice da wadannan kamfanoni suka mallaka ya karu daga kashi 43.% na 2019 zuwa kashi 55.5%, kuma cikin shekaru 6 a jere, sun zama bangare mafi girma a nan kasar Sin ta fuskar cinikin shige da fice. A matsayinsu na jigon cinikin shige da fice, kamfanonin Sin masu zaman kansu sun taka rawar gani a bangaren ba da tabbaci ga tsarin samar da kayayyaki a duniya. (Amina Xu)