Bisa labarin da hukumar ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, an ce, a halin yanzu, a cikin kayayyaki masu lambar kira da aka kirkiro a kasar Sin, kamfanoni sun samar da kashi fiye da 70 cikin dari, wato yawan kayayyakin masu lambar kira da kamfanoni suka samar ya zarce miliyan 3. Kamfanonin Sin sun kara kirkiro sabbin kayayyaki masu lambar kira, da yin amfani da su yadda ya kamata.
Wani jami’in hukumar ya bayyana cewa, a kwanakin baya, hukumar ikon mallakar fasaha ta kasar Sin da sauran hukumomin da abin ya shafa sun yi hadin gwiwa wajen gabatar da shirin raya kamfanoni kanana da matsakaita ta hanyar kirkiro kayayyaki masu lambar kira, wanda ya sa kaimi ga kamfanoni kanana da matsakaita masu karfin yin kirkire-kirkire da su dauki matakan samar da hidima da horar da kwararru don sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci ta hanyar kirkiro kayayyakkin masu lambar kira.
Jami’in ya kara da cewa, yawan kayayyaki masu lambar kira da kamfanonin Sin suka kirkiro tare da yin amfani da su a zahiri a shekarar 2023 ya kai kashi 51.3 cikin dari, wanda ya zarce kashi 50 cikin dari karo na farko, da kuma ya karu da kashi 3.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2022, da kiyaye samun karuwar a shekaru 5 a jere. (Zainab Zhang)