Shugaban Kamfanin taki na RaRa “Agrobet”, MD. Alhaji Abdullahi Rara ya bayyana cewa kamfanonin taki na cikin gida Nijeriya za su iya taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa manona.
A cewarsa, harkar noma yana tafiya daidai a Jihar Jigawa sakamako yadda gwamnati take bakin kokarinta, sannan kamfanoni na waje da na gida irin nasu sun shigo suna taimaka wa manoma.
- Mutum Biyu Sun FaÉ—a Komar ‘Yansanda Bisa Zargin Sata A Gombe
- Buratai Ya ÆŠauki ÆŠamarar ÆŠaga Likkafar Fasaha a Nijeriya
Ya ce kusan kowane gari a lungu da sako na cikin jihar babu inda ba sa ba su tallafi da taimako na taki idan sun gama noma su biya. Ya ce da ba dun suna shiga ko’ina suna taimaka wa manoma ba, da manoma sun shiga wahalar karancin taki da zai ya ci musu tuwo a kwarya.
Haka kuma ya ce su a nasu tsarin na kamfanoni na cikin gida da suke taimakon manoma a Jihar Jigawa suna da tsare-tsare da gwamnati ba su da shi, su sun tsara da lauyoyinsu da sauran duk wani mai ruwa da tsaki ta yadda abin da zai tafi daidai kuma komai yana tafiya yanda ya kamata ba tare da wasu matsaloli ba.
MD. Abdullahi ya ce ita gwamnati a tsare-tsarenta ba ta neman kamfanoni, kuma rashin neman kamfanoni ke hana samun nasara wajen tsara yanda za a tallafa wa manoma na samun saukin taki da yanda za su biya.