Babban bankin Nijeriya (CBN) ya ce kananan Manoma kimanin 31,666 suka ci gajiyar shirin lamuni da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.92 a karkashin asusun bayar da lamuni na aikin gona (ACGSF) duk da cewa manoman da ke cin gajiyar shirin sun yi kira da a kara musu yawan kudin lamunin.
ACGSF, Shirin lamunin Manoma ne na Babban bankin Nijeriya wanda aka kafa a cikin shekarar 1977, an yi shi ne don taimakawa wajen samar da kudade ga manoma a kasar.
Da yake jawabi a wajen bikin karrama manoman ACGSF da aka gudanar a dakin taro Na CBN da ke Legas, mukaddashin mai kula da reshen bankin Apex, Nnaemeka Ukanyirioha, ya bayyana cewa, duk da kalubalen da kasar nan ta fuskanta a baya-bayan nan, ta ci gaba da tabbatar da samar da hanyoyin bada lamunin kudi da za a iya amfani da su wajen gudanar da aikin noma.
Ya ce, a karkashin shirin ACGSF, CBN ya ba da “lamuni 31,666 da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.92” a shekarar 2021.
Ya bayyana cewa an ba da lambar yabon ne don karrama wadanda suka shiga cikin shirin da suka nuna kwazo da himma wajen bunkasa Kasar mu ta fannin noma duk da dimbin kalubalen da aka fuskanta.
“Shekarar da ta gabata ta kasance da kalubale musamman ga bangaren kasuwanci Wanda yanzun ake kokarin murmurewa daga cutar Korona da ta barke a duniya.”